نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4834 | 53 | 50 | وأنه أهلك عادا الأولى |
| | | Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko. |
|
4835 | 53 | 51 | وثمود فما أبقى |
| | | Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba. |
|
4836 | 53 | 52 | وقوم نوح من قبل إنهم كانوا هم أظلم وأطغى |
| | | Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai. |
|
4837 | 53 | 53 | والمؤتفكة أهوى |
| | | Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su. |
|
4838 | 53 | 54 | فغشاها ما غشى |
| | | Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su. |
|
4839 | 53 | 55 | فبأي آلاء ربك تتمارى |
| | | To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka? |
|
4840 | 53 | 56 | هذا نذير من النذر الأولى |
| | | wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko. |
|
4841 | 53 | 57 | أزفت الآزفة |
| | | Makusanciya fa, tã yi kusa. |
|
4842 | 53 | 58 | ليس لها من دون الله كاشفة |
| | | Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta. |
|
4843 | 53 | 59 | أفمن هذا الحديث تعجبون |
| | | Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki? |
|