نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4816 | 53 | 32 | الذين يجتنبون كبائر الإثم والفواحش إلا اللمم إن ربك واسع المغفرة هو أعلم بكم إذ أنشأكم من الأرض وإذ أنتم أجنة في بطون أمهاتكم فلا تزكوا أنفسكم هو أعلم بمن اتقى |
| | | Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa. |
|
4817 | 53 | 33 | أفرأيت الذي تولى |
| | | Shin, ka ga wannan da ya jũya baya? |
|
4818 | 53 | 34 | وأعطى قليلا وأكدى |
| | | Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa? |
|
4819 | 53 | 35 | أعنده علم الغيب فهو يرى |
| | | Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin? |
|
4820 | 53 | 36 | أم لم ينبأ بما في صحف موسى |
| | | Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã? |
|
4821 | 53 | 37 | وإبراهيم الذي وفى |
| | | Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari? |
|
4822 | 53 | 38 | ألا تزر وازرة وزر أخرى |
| | | Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani. |
|
4823 | 53 | 39 | وأن ليس للإنسان إلا ما سعى |
| | | Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata. |
|
4824 | 53 | 40 | وأن سعيه سوف يرى |
| | | Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi. |
|
4825 | 53 | 41 | ثم يجزاه الجزاء الأوفى |
| | | Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni? |
|