نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4805 | 53 | 21 | ألكم الذكر وله الأنثى |
| | | Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace? |
|
4806 | 53 | 22 | تلك إذا قسمة ضيزى |
| | | Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe. |
|
4807 | 53 | 23 | إن هي إلا أسماء سميتموها أنتم وآباؤكم ما أنزل الله بها من سلطان إن يتبعون إلا الظن وما تهوى الأنفس ولقد جاءهم من ربهم الهدى |
| | | Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton). |
|
4808 | 53 | 24 | أم للإنسان ما تمنى |
| | | Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri? |
|
4809 | 53 | 25 | فلله الآخرة والأولى |
| | | To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure). |
|
4810 | 53 | 26 | وكم من ملك في السماوات لا تغني شفاعتهم شيئا إلا من بعد أن يأذن الله لمن يشاء ويرضى |
| | | Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda. |
|
4811 | 53 | 27 | إن الذين لا يؤمنون بالآخرة ليسمون الملائكة تسمية الأنثى |
| | | Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace. |
|
4812 | 53 | 28 | وما لهم به من علم إن يتبعون إلا الظن وإن الظن لا يغني من الحق شيئا |
| | | Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya. |
|
4813 | 53 | 29 | فأعرض عن من تولى عن ذكرنا ولم يرد إلا الحياة الدنيا |
| | | Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambatonMu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya). |
|
4814 | 53 | 30 | ذلك مبلغهم من العلم إن ربك هو أعلم بمن ضل عن سبيله وهو أعلم بمن اهتدى |
| | | Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya. |
|