نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
481 | 3 | 188 | لا تحسبن الذين يفرحون بما أتوا ويحبون أن يحمدوا بما لم يفعلوا فلا تحسبنهم بمفازة من العذاب ولهم عذاب أليم |
| | | Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bãyar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikatã ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsĩra daga azãba. Kuma suna da azãba mai raɗadi. |
|
482 | 3 | 189 | ولله ملك السماوات والأرض والله على كل شيء قدير |
| | | Kuma ga Allah mulkin sammai da ƙasa yake. Kuma Allah, a kan kõme, Mai ĩkon yi ne. |
|
483 | 3 | 190 | إن في خلق السماوات والأرض واختلاف الليل والنهار لآيات لأولي الألباب |
| | | Lalle ne, a cikin halittar sammai da ƙasa da sãɓãwar dare da yini akwai ãyõyi ga ma'abũta hankali. |
|
484 | 3 | 191 | الذين يذكرون الله قياما وقعودا وعلى جنوبهم ويتفكرون في خلق السماوات والأرض ربنا ما خلقت هذا باطلا سبحانك فقنا عذاب النار |
| | | Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sãsanninsu, kuma suna tunãni a kan halittar sammai da ƙasa: "Yã Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Sabõda haka Ka tsare mu daga azãbar wuta. |
|
485 | 3 | 192 | ربنا إنك من تدخل النار فقد أخزيته وما للظالمين من أنصار |
| | | "Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai, wanda Ka shigar a cikin wuta to, haƙĩƙa, Ka tozarta shi kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai. |
|
486 | 3 | 193 | ربنا إننا سمعنا مناديا ينادي للإيمان أن آمنوا بربكم فآمنا ربنا فاغفر لنا ذنوبنا وكفر عنا سيئاتنا وتوفنا مع الأبرار |
| | | "Yã Ubangijinmu! Lalle ne mũ mun ji Mai kira yanã kira zuwa ga ĩmãni cẽwa, 'Ku yi ĩmãni da Ubangijinku.' Sai muka yi ĩmãni. Yã Ubangijinmu! Sabõda haka Ka gãfarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyãgun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rãyukanmu tãre da mutãnen kirki. |
|
487 | 3 | 194 | ربنا وآتنا ما وعدتنا على رسلك ولا تخزنا يوم القيامة إنك لا تخلف الميعاد |
| | | "Yã Ubangijinmu! Ka bã mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Rãnar ¡iyãma. Lalle ne Kai, bã Ka sãɓãwar alkawari." |
|
488 | 3 | 195 | فاستجاب لهم ربهم أني لا أضيع عمل عامل منكم من ذكر أو أنثى بعضكم من بعض فالذين هاجروا وأخرجوا من ديارهم وأوذوا في سبيلي وقاتلوا وقتلوا لأكفرن عنهم سيئاتهم ولأدخلنهم جنات تجري من تحتها الأنهار ثوابا من عند الله والله عنده حسن الثواب |
| | | Sabõda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cẽwa, "Lallene Nĩ bã zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sãshenku daga sãshe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidãjensu, kuma aka cũtar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yãƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudãna daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako. |
|
489 | 3 | 196 | لا يغرنك تقلب الذين كفروا في البلاد |
| | | Kada jujjuyawar waɗanda suka kãfirta a cikin garũruwa ta rũɗe ka. |
|
490 | 3 | 197 | متاع قليل ثم مأواهم جهنم وبئس المهاد |
| | | Jin dãɗi ne kaɗan sa'an nan makõmarsu Jahannama ce, kuma tir da shimfiɗa ita! |
|