نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4793 | 53 | 9 | فكان قاب قوسين أو أدنى |
| | | Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa. |
|
4794 | 53 | 10 | فأوحى إلى عبده ما أوحى |
| | | Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa). |
|
4795 | 53 | 11 | ما كذب الفؤاد ما رأى |
| | | Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba. |
|
4796 | 53 | 12 | أفتمارونه على ما يرى |
| | | Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani? |
|
4797 | 53 | 13 | ولقد رآه نزلة أخرى |
| | | Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa. |
|
4798 | 53 | 14 | عند سدرة المنتهى |
| | | A wurin da magaryar tuƙẽwa take. |
|
4799 | 53 | 15 | عندها جنة المأوى |
| | | A inda taken, nan Aljannar makoma take. |
|
4800 | 53 | 16 | إذ يغشى السدرة ما يغشى |
| | | Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta. |
|
4801 | 53 | 17 | ما زاغ البصر وما طغى |
| | | Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba. |
|
4802 | 53 | 18 | لقد رأى من آيات ربه الكبرى |
| | | Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa. |
|