نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4774 | 52 | 39 | أم له البنات ولكم البنون |
| | | Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne? |
|
4775 | 52 | 40 | أم تسألهم أجرا فهم من مغرم مثقلون |
| | | Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar? |
|
4776 | 52 | 41 | أم عندهم الغيب فهم يكتبون |
| | | Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa? |
|
4777 | 52 | 42 | أم يريدون كيدا فالذين كفروا هم المكيدون |
| | | Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi. |
|
4778 | 52 | 43 | أم لهم إله غير الله سبحان الله عما يشركون |
| | | Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki! |
|
4779 | 52 | 44 | وإن يروا كسفا من السماء ساقطا يقولوا سحاب مركوم |
| | | Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna. |
|
4780 | 52 | 45 | فذرهم حتى يلاقوا يومهم الذي فيه يصعقون |
| | | To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa. |
|
4781 | 52 | 46 | يوم لا يغني عنهم كيدهم شيئا ولا هم ينصرون |
| | | Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su. |
|
4782 | 52 | 47 | وإن للذين ظلموا عذابا دون ذلك ولكن أكثرهم لا يعلمون |
| | | Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba. |
|
4783 | 52 | 48 | واصبر لحكم ربك فإنك بأعيننا وسبح بحمد ربك حين تقوم |
| | | Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu). |
|