نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4771 | 52 | 36 | أم خلقوا السماوات والأرض بل لا يوقنون |
| | | Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba. |
|
4772 | 52 | 37 | أم عندهم خزائن ربك أم هم المصيطرون |
| | | Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya? |
|
4773 | 52 | 38 | أم لهم سلم يستمعون فيه فليأت مستمعهم بسلطان مبين |
| | | Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne. |
|
4774 | 52 | 39 | أم له البنات ولكم البنون |
| | | Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne? |
|
4775 | 52 | 40 | أم تسألهم أجرا فهم من مغرم مثقلون |
| | | Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar? |
|
4776 | 52 | 41 | أم عندهم الغيب فهم يكتبون |
| | | Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa? |
|
4777 | 52 | 42 | أم يريدون كيدا فالذين كفروا هم المكيدون |
| | | Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi. |
|
4778 | 52 | 43 | أم لهم إله غير الله سبحان الله عما يشركون |
| | | Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki! |
|
4779 | 52 | 44 | وإن يروا كسفا من السماء ساقطا يقولوا سحاب مركوم |
| | | Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna. |
|
4780 | 52 | 45 | فذرهم حتى يلاقوا يومهم الذي فيه يصعقون |
| | | To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa. |
|