نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4752 | 52 | 17 | إن المتقين في جنات ونعيم |
| | | Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima. |
|
4753 | 52 | 18 | فاكهين بما آتاهم ربهم ووقاهم ربهم عذاب الجحيم |
| | | Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm. |
|
4754 | 52 | 19 | كلوا واشربوا هنيئا بما كنتم تعملون |
| | | (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa." |
|
4755 | 52 | 20 | متكئين على سرر مصفوفة وزوجناهم بحور عين |
| | | Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu. |
|
4756 | 52 | 21 | والذين آمنوا واتبعتهم ذريتهم بإيمان ألحقنا بهم ذريتهم وما ألتناهم من عملهم من شيء كل امرئ بما كسب رهين |
| | | Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta. |
|
4757 | 52 | 22 | وأمددناهم بفاكهة ولحم مما يشتهون |
| | | Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari. |
|
4758 | 52 | 23 | يتنازعون فيها كأسا لا لغو فيها ولا تأثيم |
| | | Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi. |
|
4759 | 52 | 24 | ويطوف عليهم غلمان لهم كأنهم لؤلؤ مكنون |
| | | Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle. |
|
4760 | 52 | 25 | وأقبل بعضهم على بعض يتساءلون |
| | | Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna. |
|
4761 | 52 | 26 | قالوا إنا كنا قبل في أهلنا مشفقين |
| | | Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro." |
|