نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4728 | 51 | 53 | أتواصوا به بل هم قوم طاغون |
| | | shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai. |
|
4729 | 51 | 54 | فتول عنهم فما أنت بملوم |
| | | Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne. |
|
4730 | 51 | 55 | وذكر فإن الذكرى تنفع المؤمنين |
| | | Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai. |
|
4731 | 51 | 56 | وما خلقت الجن والإنس إلا ليعبدون |
| | | Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini. |
|
4732 | 51 | 57 | ما أريد منهم من رزق وما أريد أن يطعمون |
| | | Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni. |
|
4733 | 51 | 58 | إن الله هو الرزاق ذو القوة المتين |
| | | Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi. |
|
4734 | 51 | 59 | فإن للذين ظلموا ذنوبا مثل ذنوب أصحابهم فلا يستعجلون |
| | | To, lalle waɗanda suka yi zãlunci sunã da masaki (na ɗĩban zunubi) kamar masakin abõkansu, sabõda haka kada su yi Mini gaggãwa. |
|
4735 | 51 | 60 | فويل للذين كفروا من يومهم الذي يوعدون |
| | | Sabõda haka, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta, daga rãnar su wadda aka yi musu alkawari. |
|
4736 | 52 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والطور |
| | | Inã rantsuwa da ¦ũr (Dũtsen Mũsã). |
|
4737 | 52 | 2 | وكتاب مسطور |
| | | Da wani littãfi rubũtacce. |
|