نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4724 | 51 | 49 | ومن كل شيء خلقنا زوجين لعلكم تذكرون |
| | | Kuma daga kõme Mun halitta nau'i biyu, watakila zã ku yi tunãni. |
|
4725 | 51 | 50 | ففروا إلى الله إني لكم منه نذير مبين |
| | | Sabõda haka ku gudu zuwa ga Allah, lalle nĩ mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. |
|
4726 | 51 | 51 | ولا تجعلوا مع الله إلها آخر إني لكم منه نذير مبين |
| | | Kuma kada ku sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, lalle nĩ, mai gargaɗi kawai ne a gare ku, mai bayyanannen gargaɗi. |
|
4727 | 51 | 52 | كذلك ما أتى الذين من قبلهم من رسول إلا قالوا ساحر أو مجنون |
| | | Kamar haka dai wani Manzo bai jẽ wa waɗanda ke gabãninsu ba fãce sun ce: "Mai sihiri ne kõ mahaukaci." |
|
4728 | 51 | 53 | أتواصوا به بل هم قوم طاغون |
| | | shin, sunã yi wa jũna wasiyya da shi ne? Ã'a, sũ dai mutãne ne mãsu girman kai. |
|
4729 | 51 | 54 | فتول عنهم فما أنت بملوم |
| | | Sai ka jũya daga barinsu, kuma kai ba abin zargi ba ne. |
|
4730 | 51 | 55 | وذكر فإن الذكرى تنفع المؤمنين |
| | | Kuma ka tunãtar, dõmin tunãtarwa tanã amfãnin mũminai. |
|
4731 | 51 | 56 | وما خلقت الجن والإنس إلا ليعبدون |
| | | Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini. |
|
4732 | 51 | 57 | ما أريد منهم من رزق وما أريد أن يطعمون |
| | | Bã Ni nufln (sãmun) wani arziki daga gare su, Bã Ni nufin su (yi Mini hidimar) ciyar da Ni. |
|
4733 | 51 | 58 | إن الله هو الرزاق ذو القوة المتين |
| | | Lalle Allah, Shĩ ne Mai azurtãwa, Mai ĩkon yi, Mai cikakken ƙarfi. |
|