نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4714 | 51 | 39 | فتولى بركنه وقال ساحر أو مجنون |
| | | Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!" |
|
4715 | 51 | 40 | فأخذناه وجنوده فنبذناهم في اليم وهو مليم |
| | | Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. |
|
4716 | 51 | 41 | وفي عاد إذ أرسلنا عليهم الريح العقيم |
| | | Kuma ga Ãdãwa, a lõkacin da Muka aika iska ƙẽƙasasshiya a kansu. |
|
4717 | 51 | 42 | ما تذر من شيء أتت عليه إلا جعلته كالرميم |
| | | Bã ta barin kõme da ta jẽ a kansa, fãce ta mayar da shi kamar rududdugaggun ƙasũsuwa. |
|
4718 | 51 | 43 | وفي ثمود إذ قيل لهم تمتعوا حتى حين |
| | | Kuma ga Samũdãwa, a lõkacin da aka ce musu: "Ku ji ɗan dãɗi har wani ɗan lõkaci," |
|
4719 | 51 | 44 | فعتوا عن أمر ربهم فأخذتهم الصاعقة وهم ينظرون |
| | | Sai suka yi girman kai ga umurnin Ubangijinsu, sabõda haka tsãwa ta kãma su, alhãli kuwa sunã kallo. |
|
4720 | 51 | 45 | فما استطاعوا من قيام وما كانوا منتصرين |
| | | Ba su kõ sãmu dãmar tsayãwa ba, kuma ba su kasance mãsu nẽman ãgaji ba. |
|
4721 | 51 | 46 | وقوم نوح من قبل إنهم كانوا قوما فاسقين |
| | | Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai. |
|
4722 | 51 | 47 | والسماء بنيناها بأيد وإنا لموسعون |
| | | Kuma sama, mun gina ta da wani irin ƙarfi, alhãli kuwa lalle Mũ ne Mãsu yalwatãwa. |
|
4723 | 51 | 48 | والأرض فرشناها فنعم الماهدون |
| | | Kuma ƙasã Mun shimfiɗa ta, To, madalla da mãsu shimfiɗãwa, Mũ, |
|