نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4706 | 51 | 31 | قال فما خطبكم أيها المرسلون |
| | | (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!" |
|
4707 | 51 | 32 | قالوا إنا أرسلنا إلى قوم مجرمين |
| | | Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi. |
|
4708 | 51 | 33 | لنرسل عليهم حجارة من طين |
| | | "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom). |
|
4709 | 51 | 34 | مسومة عند ربك للمسرفين |
| | | "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna." |
|
4710 | 51 | 35 | فأخرجنا من كان فيها من المؤمنين |
| | | Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai. |
|
4711 | 51 | 36 | فما وجدنا فيها غير بيت من المسلمين |
| | | Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi. |
|
4712 | 51 | 37 | وتركنا فيها آية للذين يخافون العذاب الأليم |
| | | Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi. |
|
4713 | 51 | 38 | وفي موسى إذ أرسلناه إلى فرعون بسلطان مبين |
| | | Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. |
|
4714 | 51 | 39 | فتولى بركنه وقال ساحر أو مجنون |
| | | Sai ya jũya bãya tãre da ƙarfinsa, kuma ya ce: "Mai sihiri ne kõ kuwa mahaukaci!" |
|
4715 | 51 | 40 | فأخذناه وجنوده فنبذناهم في اليم وهو مليم |
| | | Sabõda haka, Muka kama shi tãre da rundunarsa, sa'an nan Muka jẽfa su a cikin tẽku, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi. |
|