نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4704 | 51 | 29 | فأقبلت امرأته في صرة فصكت وجهها وقالت عجوز عقيم |
| | | Sai matarsa ta fuskanta cikin ƙyallõwa, har ta mari fuskarta kuma ta ce: "Tsõhuwa bakarãriya (zã ta haihu)!" |
|
4705 | 51 | 30 | قالوا كذلك قال ربك إنه هو الحكيم العليم |
| | | Suka ce: "Kamar haka Ubangijinki Ya faɗa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai hikima, Mai ilmi." |
|
4706 | 51 | 31 | قال فما خطبكم أيها المرسلون |
| | | (Ibrãĩm) ya ce: "To mẽne ne babban al'almarinku, yã kũ Manzanni!" |
|
4707 | 51 | 32 | قالوا إنا أرسلنا إلى قوم مجرمين |
| | | Suka ce: "Lalle mũ, an aike mu zuwa ga waɗansu mutãne, mãsu laifi. |
|
4708 | 51 | 33 | لنرسل عليهم حجارة من طين |
| | | "Dõmin mu saka musu waɗansu duwãtsu na wani yumɓu (bom). |
|
4709 | 51 | 34 | مسومة عند ربك للمسرفين |
| | | "Waɗanda aka yi wa alãma daga wajen Ubangijinka, dõmin mãsu ɓarna." |
|
4710 | 51 | 35 | فأخرجنا من كان فيها من المؤمنين |
| | | Sa'an, nan Muka fitar da wanda ya kasance a cikinta daga mũminai. |
|
4711 | 51 | 36 | فما وجدنا فيها غير بيت من المسلمين |
| | | Sai dai ba mu sãmu ba, a cikinta, fãce gida guda na Musulmi. |
|
4712 | 51 | 37 | وتركنا فيها آية للذين يخافون العذاب الأليم |
| | | Kuma Muka bar wata ãyã, a cikinta, ga waɗanda ke jin tsõron azãba, mai raɗaɗi. |
|
4713 | 51 | 38 | وفي موسى إذ أرسلناه إلى فرعون بسلطان مبين |
| | | Kuma ga Mũsã, a lõkacin da Muka aiko shi zuwa ga Fir'auna da wani dalĩli bayyananne. |
|