نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4694 | 51 | 19 | وفي أموالهم حق للسائل والمحروم |
| | | Kuma a cikin dũkiyarsu akwai hakki ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hana wa rõƙo. |
|
4695 | 51 | 20 | وفي الأرض آيات للموقنين |
| | | Kuma a cikin ƙasã akwai ãyõyi ga mãsu yaƙĩni. |
|
4696 | 51 | 21 | وفي أنفسكم أفلا تبصرون |
| | | Kuma a cikin rãyukanku (akwai ãyõyi). To, bã zã ku dũbã ba? |
|
4697 | 51 | 22 | وفي السماء رزقكم وما توعدون |
| | | Kuma a cikin sama arzikinku (yake fitõwa) da abin da ake yi muku alkawari. |
|
4698 | 51 | 23 | فورب السماء والأرض إنه لحق مثل ما أنكم تنطقون |
| | | To, kuma Ina rantsuwa da Ubangijin sama da ƙasã, lalle shĩ (abin da ake yi muku alkawari), haƙĩƙa gaskiya ne, kamar abin da kuka zamo kunã karantãwa na magana, |
|
4699 | 51 | 24 | هل أتاك حديث ضيف إبراهيم المكرمين |
| | | Shin, lãbãrin Bãƙin Ibrãhĩm, waɗanda aka girmama, ya zo maka? |
|
4700 | 51 | 25 | إذ دخلوا عليه فقالوا سلاما قال سلام قوم منكرون |
| | | A lõkacin da suka shiga gare shi, sai suka yi sallama; ya ce "Aminci ya tabbata a gare ku, mutãne bãƙi!" |
|
4701 | 51 | 26 | فراغ إلى أهله فجاء بعجل سمين |
| | | Sai ya jũya zuwa ga iyãlinsa, sa'an nan ya zo da maraƙi tutturna, |
|
4702 | 51 | 27 | فقربه إليهم قال ألا تأكلون |
| | | Sai ya kusantar da shi zuwa gare su, ya ce: "Bã zã ku ci ba?" |
|
4703 | 51 | 28 | فأوجس منهم خيفة قالوا لا تخف وبشروه بغلام عليم |
| | | Sai ya ji tsõro daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro." Kuma suka yi masa bushãra da (haihuwar) wani yaro mai ilmi. |
|