نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4681 | 51 | 6 | وإن الدين لواقع |
| | | Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne |
|
4682 | 51 | 7 | والسماء ذات الحبك |
| | | Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo). |
|
4683 | 51 | 8 | إنكم لفي قول مختلف |
| | | Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani). |
|
4684 | 51 | 9 | يؤفك عنه من أفك |
| | | Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya). |
|
4685 | 51 | 10 | قتل الخراصون |
| | | An la'ani mãsu ƙiri-faɗi. |
|
4686 | 51 | 11 | الذين هم في غمرة ساهون |
| | | Waɗanda suke shagala a cikin zurfin jãhilci. |
|
4687 | 51 | 12 | يسألون أيان يوم الدين |
| | | Sunã tambaya: "Yaushe ne rãnar sakamako zã ta auku?" |
|
4688 | 51 | 13 | يوم هم على النار يفتنون |
| | | Ranar da suke a kan wuta anã fitinar su. |
|
4689 | 51 | 14 | ذوقوا فتنتكم هذا الذي كنتم به تستعجلون |
| | | (A ce musu): "Ku ɗanɗani fitinarku, wannan shĩ ne abin da kuka kasance kunã nẽman zuwansa da gaggãwa." |
|
4690 | 51 | 15 | إن المتقين في جنات وعيون |
| | | Lalle mãsu taƙawa, sunã a cikin lambunan itãce da marẽmari. |
|