نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4676 | 51 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والذاريات ذروا |
| | | Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa. |
|
4677 | 51 | 2 | فالحاملات وقرا |
| | | Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa). |
|
4678 | 51 | 3 | فالجاريات يسرا |
| | | Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi. |
|
4679 | 51 | 4 | فالمقسمات أمرا |
| | | Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah). |
|
4680 | 51 | 5 | إنما توعدون لصادق |
| | | Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne. |
|
4681 | 51 | 6 | وإن الدين لواقع |
| | | Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne |
|
4682 | 51 | 7 | والسماء ذات الحبك |
| | | Inã rantsuwa da samã ma'abũciyar hanyõyi (na tafiyar taurãri da sautin rediyo). |
|
4683 | 51 | 8 | إنكم لفي قول مختلف |
| | | Lalle kũ, haƙĩƙa, kunã cikin magana mai sãɓa wa juna (game da Alƙur'ani). |
|
4684 | 51 | 9 | يؤفك عنه من أفك |
| | | Anã karkatar da wanda aka jũyar (daga gaskiya). |
|
4685 | 51 | 10 | قتل الخراصون |
| | | An la'ani mãsu ƙiri-faɗi. |
|