نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4672 | 50 | 42 | يوم يسمعون الصيحة بالحق ذلك يوم الخروج |
| | | Rãnar da suke saurãron tsãwa da gaskiya. Wancan shĩ ne yinin fita (daga kabari). |
|
4673 | 50 | 43 | إنا نحن نحيي ونميت وإلينا المصير |
| | | Lalle Mũ ne haƙĩƙa, Mu ne ke rãyarwa, kuma Mũ ne ke kashẽwa, kuma zuwa gare Mu kawai ne makõmar take. |
|
4674 | 50 | 44 | يوم تشقق الأرض عنهم سراعا ذلك حشر علينا يسير |
| | | Rãnar da ƙasã ke tsattsãgẽwa daga gare su, sunã mãsu gaggãwa. Wancan tãrãwar mutãne ne, mai sauƙi a gare Mu. |
|
4675 | 50 | 45 | نحن أعلم بما يقولون وما أنت عليهم بجبار فذكر بالقرآن من يخاف وعيد |
| | | Mũ ne mafi sani game da abin da suke faɗi, kuma bã zã ka zama mai tĩlasta su ba. Sabõda haka ka tunatar game da Alƙur'ani, ga wanda ke tsõron ƙyacewaTa. |
|
4676 | 51 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم والذاريات ذروا |
| | | Inã rantsuwa da iskõki mãsu shẽkar abũbuwa, shẽƙẽwa. |
|
4677 | 51 | 2 | فالحاملات وقرا |
| | | Sa'an nan da girãgizai mãsu ɗaukar nauyi (na ruwa). |
|
4678 | 51 | 3 | فالجاريات يسرا |
| | | Sa'an nan da jirãge mãsu gudãna (a kan ruwa) da sauƙi. |
|
4679 | 51 | 4 | فالمقسمات أمرا |
| | | Sa'an nan da Malã'iku mãsu rabon al'amari (bisa umurnin Allah). |
|
4680 | 51 | 5 | إنما توعدون لصادق |
| | | Lalle abin da ake yi muku alkawari (da zuwansa), haƙĩƙa gaskiya ne. |
|
4681 | 51 | 6 | وإن الدين لواقع |
| | | Kuma lalle sakamako (ga ayyukanku), haƙĩƙa, mai aukuwa ne |
|