نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4662 | 50 | 32 | هذا ما توعدون لكل أواب حفيظ |
| | | "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa). |
|
4663 | 50 | 33 | من خشي الرحمن بالغيب وجاء بقلب منيب |
| | | "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali." |
|
4664 | 50 | 34 | ادخلوها بسلام ذلك يوم الخلود |
| | | (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama." |
|
4665 | 50 | 35 | لهم ما يشاءون فيها ولدينا مزيد |
| | | Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima, |
|
4666 | 50 | 36 | وكم أهلكنا قبلهم من قرن هم أشد منهم بطشا فنقبوا في البلاد هل من محيص |
| | | Kuma da yawa Muka halakar, a gabãninsu, (mutãnen yanzu) ɗaga waɗansu al'ummomi, (waɗanda suke) sũ ne mafi ƙarfin damƙa daga gare su, sa'an nan suka yi bincike a cikin ƙasãshe: 'Kõ akwai wurin tsĩra'? (Babu). |
|
4667 | 50 | 37 | إن في ذلك لذكرى لمن كان له قلب أو ألقى السمع وهو شهيد |
| | | Lalle ne, a cikin wancan, akwai tunãtarwa ga wanda zũciyarsa ta kasance gare shi, kõ kuwa ya jẽfa saurãro, alhãli kuwa yanã halarce (da hankalinsa). |
|
4668 | 50 | 38 | ولقد خلقنا السماوات والأرض وما بينهما في ستة أيام وما مسنا من لغوب |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu, a cikin kwãnaki shida, alhãli wata'yar wahala ba ta shãfe Mu ba. |
|
4669 | 50 | 39 | فاصبر على ما يقولون وسبح بحمد ربك قبل طلوع الشمس وقبل الغروب |
| | | Sabõda haka, ka yi haƙuri a kan abin da suke fadã, kuma ka yi tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinka (watau ka yi salla) a gabãnin fitõwar rãnã da gabãnin ɓacẽwarta. |
|
4670 | 50 | 40 | ومن الليل فسبحه وأدبار السجود |
| | | Kuma daga dare, sai ka yi tasbĩhi a gare Shi da bãyan sujada. |
|
4671 | 50 | 41 | واستمع يوم يناد المناد من مكان قريب |
| | | Kuma ka saurãra a rãnar da mai kira ke yin kira daga wuri makusanci. |
|