نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4656 | 50 | 26 | الذي جعل مع الله إلها آخر فألقياه في العذاب الشديد |
| | | "Wanda ya sanya, tãre da Allah wani abin bautãwa na dabam, sabõda haka kujẽfa shi a cikin azãba mai tsanani." |
|
4657 | 50 | 27 | قال قرينه ربنا ما أطغيته ولكن كان في ضلال بعيد |
| | | Abõkin haɗinsa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Ban sanya shi girman kai ba, kuma amma ya kasance a cikin ɓata mai nĩsa." |
|
4658 | 50 | 28 | قال لا تختصموا لدي وقد قدمت إليكم بالوعيد |
| | | Ya ce: "Kada ku yi husũma a wuriNa, alhãli Na gabãtar da ƙyacewa zuwa gare ku." |
|
4659 | 50 | 29 | ما يبدل القول لدي وما أنا بظلام للعبيد |
| | | "Ba a musanya magana a wuriNa, Kuma Ban zama Mai zãlunci ba ga bãyiNa." |
|
4660 | 50 | 30 | يوم نقول لجهنم هل امتلأت وتقول هل من مزيد |
| | | Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe, akwai wani ƙãri?" |
|
4661 | 50 | 31 | وأزلفت الجنة للمتقين غير بعيد |
| | | Kuma a kusantar dã Aljanna ga mãsu taƙawa, ba da nĩsa ba. |
|
4662 | 50 | 32 | هذا ما توعدون لكل أواب حفيظ |
| | | "Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi da shi ga dukan mai yawan kõmawa ga Allah, mai tsarewar (umurninSa). |
|
4663 | 50 | 33 | من خشي الرحمن بالغيب وجاء بقلب منيب |
| | | "Wanda ya ji tsõron Mai rahama a fake, kuma ya zo da wata irin zũciya mai tawakkali." |
|
4664 | 50 | 34 | ادخلوها بسلام ذلك يوم الخلود |
| | | (A ce musu) "Ku shige ta da aminci, waccan ita ce rãnar dawwama." |
|
4665 | 50 | 35 | لهم ما يشاءون فيها ولدينا مزيد |
| | | Sunã da abin da suke so a cikinta, kuma tãre da Mũ akwai ƙãrin ni'ima, |
|