نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4642 | 50 | 12 | كذبت قبلهم قوم نوح وأصحاب الرس وثمود |
| | | Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu (mutãnen yanzu) da ma'abũta Rassi, da Samũdãwa. |
|
4643 | 50 | 13 | وعاد وفرعون وإخوان لوط |
| | | Da Ãdãwa da Fir'auna da 'yan'uwan Lũɗu. |
|
4644 | 50 | 14 | وأصحاب الأيكة وقوم تبع كل كذب الرسل فحق وعيد |
| | | Da ma'abũta ƙunci da mutãnen Tubba'u, kõwanensu ya ƙaryata Manzanni, sai ƙyacẽwaTa ta tabbata. |
|
4645 | 50 | 15 | أفعيينا بالخلق الأول بل هم في لبس من خلق جديد |
| | | Shin, to, Mun kãsa ne game da halittar farko? Ã'a, su sunã a cikin rikici daga halitta sãbuwa. |
|
4646 | 50 | 16 | ولقد خلقنا الإنسان ونعلم ما توسوس به نفسه ونحن أقرب إليه من حبل الوريد |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta mutum kuma Mun san abin da ransa ke yin waswãsi da shi, kuma Mũ ne mafi kusanta zuwa gare shi daga lakar jannayẽnsa. |
|
4647 | 50 | 17 | إذ يتلقى المتلقيان عن اليمين وعن الشمال قعيد |
| | | A lõkacin da mãsu haɗuwa biyu suke haɗuwa daga dãma, kuma daga hagu akwai wani (malã'ika) zaunanne. |
|
4648 | 50 | 18 | ما يلفظ من قول إلا لديه رقيب عتيد |
| | | Bã ya lafazi da wata magana fãce a lĩƙe da shi akwai mai tsaro halartacce. |
|
4649 | 50 | 19 | وجاءت سكرة الموت بالحق ذلك ما كنت منه تحيد |
| | | Kuma mãyen mutuwa ya jẽ da gaskiya. Wannan shĩ ne abin da ka kasance daga gare shi kanã bijirẽwa. |
|
4650 | 50 | 20 | ونفخ في الصور ذلك يوم الوعيد |
| | | Kuma aka hũra a cikin ƙaho. Wancan yinin ƙyacẽwar ne fa. |
|
4651 | 50 | 21 | وجاءت كل نفس معها سائق وشهيد |
| | | Kuma kõwane rai ya zo, tãre da shi akwai mai kõra da mai shaida. |
|