نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4590 | 48 | 7 | ولله جنود السماوات والأرض وكان الله عزيزا حكيما |
| | | Rundunõnin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, kuma Allah Ya kasance Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
4591 | 48 | 8 | إنا أرسلناك شاهدا ومبشرا ونذيرا |
| | | Lalle Mũ Mun aike ka, kanã mai shaida, kuma mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi. |
|
4592 | 48 | 9 | لتؤمنوا بالله ورسوله وتعزروه وتوقروه وتسبحوه بكرة وأصيلا |
| | | Dõmin ku yi ĩmani da Allah da ManzonSa, kuma ku ƙarfafa shi, kuma ku girmama Shi, kuma ku tsarkake Shi (Allah) sãfiya da maraice. |
|
4593 | 48 | 10 | إن الذين يبايعونك إنما يبايعون الله يد الله فوق أيديهم فمن نكث فإنما ينكث على نفسه ومن أوفى بما عاهد عليه الله فسيؤتيه أجرا عظيما |
| | | Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a, Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, (Allah) zai kãwo masa ijãra mai girma. |
|
4594 | 48 | 11 | سيقول لك المخلفون من الأعراب شغلتنا أموالنا وأهلونا فاستغفر لنا يقولون بألسنتهم ما ليس في قلوبهم قل فمن يملك لكم من الله شيئا إن أراد بكم ضرا أو أراد بكم نفعا بل كان الله بما تعملون خبيرا |
| | | Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa zã su ce maka, "Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara." Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: "To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma (idan) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa." |
|
4595 | 48 | 12 | بل ظننتم أن لن ينقلب الرسول والمؤمنون إلى أهليهم أبدا وزين ذلك في قلوبكم وظننتم ظن السوء وكنتم قوما بورا |
| | | Ã'a kun yi zaton Annabi da mũminai, bã za su kõmo zuwa ga iyãlansu ba, har abada. Kuma an ƙawãta wannan (tunãni) a cikin zukãtanku, kuma kun yi zato, zaton mugunta, kuma kun kasance mutãne halakakku. |
|
4596 | 48 | 13 | ومن لم يؤمن بالله ورسوله فإنا أعتدنا للكافرين سعيرا |
| | | Kuma wanda bai yi ĩmãni da Allah da kuma Manzonsa ba, to, lalle Mũ, Mun yi tattalin wutã mai tsananin ƙũna, dõmin kafirai. |
|
4597 | 48 | 14 | ولله ملك السماوات والأرض يغفر لمن يشاء ويعذب من يشاء وكان الله غفورا رحيما |
| | | Mulkin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, Yanã gãfartawa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so alhãli kuwa Allah Ya kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
|
4598 | 48 | 15 | سيقول المخلفون إذا انطلقتم إلى مغانم لتأخذوها ذرونا نتبعكم يريدون أن يبدلوا كلام الله قل لن تتبعونا كذلكم قال الله من قبل فسيقولون بل تحسدوننا بل كانوا لا يفقهون إلا قليلا |
| | | Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi dõmin ku karɓo su, "Ku bar mu, mu bĩ ku." Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: "Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka." Sa'an nan zã su ce: "Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne." Ã'a, sun kasance bã su fahimtar (abũbuwa) sai kaɗan. |
|
4599 | 48 | 16 | قل للمخلفين من الأعراب ستدعون إلى قوم أولي بأس شديد تقاتلونهم أو يسلمون فإن تطيعوا يؤتكم الله أجرا حسنا وإن تتولوا كما توليتم من قبل يعذبكم عذابا أليما |
| | | Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: "Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne mãsu tsananin yãƙi (dõmin) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi." |
|