نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
459 | 3 | 166 | وما أصابكم يوم التقى الجمعان فبإذن الله وليعلم المؤمنين |
| | | Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin (Allah) Ya san mũminai (na gaskiya). |
|
460 | 3 | 167 | وليعلم الذين نافقوا وقيل لهم تعالوا قاتلوا في سبيل الله أو ادفعوا قالوا لو نعلم قتالا لاتبعناكم هم للكفر يومئذ أقرب منهم للإيمان يقولون بأفواههم ما ليس في قلوبهم والله أعلم بما يكتمون |
| | | Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe." Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa. |
|
461 | 3 | 168 | الذين قالوا لإخوانهم وقعدوا لو أطاعونا ما قتلوا قل فادرءوا عن أنفسكم الموت إن كنتم صادقين |
| | | Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya." |
|
462 | 3 | 169 | ولا تحسبن الذين قتلوا في سبيل الله أمواتا بل أحياء عند ربهم يرزقون |
| | | Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu. Ana ciyar da su. |
|
463 | 3 | 170 | فرحين بما آتاهم الله من فضله ويستبشرون بالذين لم يلحقوا بهم من خلفهم ألا خوف عليهم ولا هم يحزنون |
| | | Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba." |
|
464 | 3 | 171 | يستبشرون بنعمة من الله وفضل وأن الله لا يضيع أجر المؤمنين |
| | | Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne, Allah bã Ya tozartar da ijãrar mũminai. |
|
465 | 3 | 172 | الذين استجابوا لله والرسول من بعد ما أصابهم القرح للذين أحسنوا منهم واتقوا أجر عظيم |
| | | Waɗanda suka karɓa kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa. |
|
466 | 3 | 173 | الذين قال لهم الناس إن الناس قد جمعوا لكم فاخشوهم فزادهم إيمانا وقالوا حسبنا الله ونعم الوكيل |
| | | Waɗanda mutãne suka ce musu: "Lalle ne, mutãne sun tãra (rundunõni) sabõda ku, don haka ku ji tsõrnsu. Sai (wannan magana) ta ƙara musu ĩmãni, kuma suka ce: "Mai isarmu Allah ne kuma mãdalla da wakili Shĩ." |
|
467 | 3 | 174 | فانقلبوا بنعمة من الله وفضل لم يمسسهم سوء واتبعوا رضوان الله والله ذو فضل عظيم |
| | | Sa'an nan sukajũya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cũta ba ta shãfe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma. |
|
468 | 3 | 175 | إنما ذلكم الشيطان يخوف أولياءه فلا تخافوهم وخافون إن كنتم مؤمنين |
| | | Wancan, Shaiɗan ne kawai yake tsõratar da, ku masõyansa. To, kada ku ji tsõronsu ku ji tsõro Na idãn kun kasance mãsu ĩmãni. |
|