نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4574 | 47 | 29 | أم حسب الذين في قلوبهم مرض أن لن يخرج الله أضغانهم |
| | | Ko kuwa waɗanda ke da wata cũta a cikin zukatansu suna zaton cẽwa Allah ba zai fitar da mugun ƙulle-ƙullen su (ga Musulunci) ba? |
|
4575 | 47 | 30 | ولو نشاء لأريناكهم فلعرفتهم بسيماهم ولتعرفنهم في لحن القول والله يعلم أعمالكم |
| | | Kuma dã Munã so, dã lalle Mun nũna maka su. To, lalle kanã sanin su game da alãmarsu. Kuma lalle kanã sanin su ga shaguɓen magana, alhali kuwa Allah Yanã sanin ayyukanku. |
|
4576 | 47 | 31 | ولنبلونكم حتى نعلم المجاهدين منكم والصابرين ونبلو أخباركم |
| | | Kuma lalle ne, Munã jarraba ku, har Mu san mãsu jihãdi daga cikinku da mãsu haƙuri kuma Muna jbrraba lãbãran ku. |
|
4577 | 47 | 32 | إن الذين كفروا وصدوا عن سبيل الله وشاقوا الرسول من بعد ما تبين لهم الهدى لن يضروا الله شيئا وسيحبط أعمالهم |
| | | Lalle ne, waɗanda suka kãfirta, kuma suka kange daga tafarkin Allah, kuma suka saɓa wa Manzon sa a bãyan shiriyar ta bayyana a gare su, bã za su cũci Allah da kõme ba, kuma zã Ya ɓãta ayyukansu. |
|
4578 | 47 | 33 | يا أيها الذين آمنوا أطيعوا الله وأطيعوا الرسول ولا تبطلوا أعمالكم |
| | | Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi ɗã'a ga Allah, kuma ku yi ɗa'a ga ManzonSa, kuma kada ku ɓãta ayyukanku. |
|
4579 | 47 | 34 | إن الذين كفروا وصدوا عن سبيل الله ثم ماتوا وهم كفار فلن يغفر الله لهم |
| | | Lalle ne waɗanda suka kãfirta sa'an nan kuma suka kange (mutãne) daga tafarkin Allah, sa'an nan suka mutu, alhãli kuwa sunã kãfirai, to, Allah bã zai yi gãfara ba a gare su. |
|
4580 | 47 | 35 | فلا تهنوا وتدعوا إلى السلم وأنتم الأعلون والله معكم ولن يتركم أعمالكم |
| | | Sabõda haka kada ku yi rauni, kuma (kada) ku yi kira zũwaga sulhi alhãli kuwa kũ ne mafiɗaukaka kuma Allah na tãre da ku, kuma bã, zai naƙasa muku ayyukanku ba. |
|
4581 | 47 | 36 | إنما الحياة الدنيا لعب ولهو وإن تؤمنوا وتتقوا يؤتكم أجوركم ولا يسألكم أموالكم |
| | | Rãyuwar dũniya, wãsã da abin shagala kawai ce, kuma idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, Allah zai kãwo muku ijarõrinku, kuma bã zai tambaye ku dũkiyarku ba. |
|
4582 | 47 | 37 | إن يسألكموها فيحفكم تبخلوا ويخرج أضغانكم |
| | | Dã Allah zai tambaye ku su (dũkiyõyin) har Ya wajabta muku bãyarwa, zã ku yi rõwa kuma Ya fitar da miyãgun ƙulle-ƙullenku. |
|
4583 | 47 | 38 | ها أنتم هؤلاء تدعون لتنفقوا في سبيل الله فمنكم من يبخل ومن يبخل فإنما يبخل عن نفسه والله الغني وأنتم الفقراء وإن تتولوا يستبدل قوما غيركم ثم لا يكونوا أمثالكم |
| | | Ga ku, ya ku waɗannan! Anã kiran ku dõmin ku ciyar ga tafarkin Allah, sa'an nan daga cikinku akwai mai yin rõwa. Kuma wanda ke yin rõwa, to, yanã yin rõwar ne ga kansa. Kuma Allah ne wadãtacce alhãli kuwa kũ fãƙĩrai ne. Kuma idan kuka jũya (daga yi Masa ɗã'a), zai musanya waɗansu mutãne waɗansunku sa'an nan bã zã su kasance kwatankwacinku ba. |
|