نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
456 | 3 | 163 | هم درجات عند الله والله بصير بما يعملون |
| | | Sũ, darajõji ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa. |
|
457 | 3 | 164 | لقد من الله على المؤمنين إذ بعث فيهم رسولا من أنفسهم يتلو عليهم آياته ويزكيهم ويعلمهم الكتاب والحكمة وإن كانوا من قبل لفي ضلال مبين |
| | | Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya. |
|
458 | 3 | 165 | أولما أصابتكم مصيبة قد أصبتم مثليها قلتم أنى هذا قل هو من عند أنفسكم إن الله على كل شيء قدير |
| | | Shin kuma a lõkacin da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne. |
|
459 | 3 | 166 | وما أصابكم يوم التقى الجمعان فبإذن الله وليعلم المؤمنين |
| | | Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin (Allah) Ya san mũminai (na gaskiya). |
|
460 | 3 | 167 | وليعلم الذين نافقوا وقيل لهم تعالوا قاتلوا في سبيل الله أو ادفعوا قالوا لو نعلم قتالا لاتبعناكم هم للكفر يومئذ أقرب منهم للإيمان يقولون بأفواههم ما ليس في قلوبهم والله أعلم بما يكتمون |
| | | Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe." Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa. |
|
461 | 3 | 168 | الذين قالوا لإخوانهم وقعدوا لو أطاعونا ما قتلوا قل فادرءوا عن أنفسكم الموت إن كنتم صادقين |
| | | Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya." |
|
462 | 3 | 169 | ولا تحسبن الذين قتلوا في سبيل الله أمواتا بل أحياء عند ربهم يرزقون |
| | | Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu. Ana ciyar da su. |
|
463 | 3 | 170 | فرحين بما آتاهم الله من فضله ويستبشرون بالذين لم يلحقوا بهم من خلفهم ألا خوف عليهم ولا هم يحزنون |
| | | Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba." |
|
464 | 3 | 171 | يستبشرون بنعمة من الله وفضل وأن الله لا يضيع أجر المؤمنين |
| | | Suna yin bushãra sabõda wata ni'ima daga Allah da wata falala. Kuma lalle ne, Allah bã Ya tozartar da ijãrar mũminai. |
|
465 | 3 | 172 | الذين استجابوا لله والرسول من بعد ما أصابهم القرح للذين أحسنوا منهم واتقوا أجر عظيم |
| | | Waɗanda suka karɓa kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bãyan mĩki ya sãme su. Akwai wata lãda mai girma ga waɗanda suka kyautata yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa. |
|