نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
454 | 3 | 161 | وما كان لنبي أن يغل ومن يغلل يأت بما غل يوم القيامة ثم توفى كل نفس ما كسبت وهم لا يظلمون |
| | | Kuma bã ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gulũlu. Wanda ya ci gulũlu zai je da abin da ya ci na gulũlun, a Rãnar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma sũ, bã zã a zãlunce su ba. |
|
455 | 3 | 162 | أفمن اتبع رضوان الله كمن باء بسخط من الله ومأواه جهنم وبئس المصير |
| | | Shin fa, wanda ya bĩbiyi yardar Allah, yana zama kamar wanda ya kõma da fushi daga Allah kuma makomarsa Jahannama ce? Kuma tir da makõma ita! |
|
456 | 3 | 163 | هم درجات عند الله والله بصير بما يعملون |
| | | Sũ, darajõji ne a wurin Allah, kuma Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatawa. |
|
457 | 3 | 164 | لقد من الله على المؤمنين إذ بعث فيهم رسولا من أنفسهم يتلو عليهم آياته ويزكيهم ويعلمهم الكتاب والحكمة وإن كانوا من قبل لفي ضلال مبين |
| | | Lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi babbar falala a kan mũminai, dõmin Yã aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ãyõyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littãfi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabãni, haƙĩƙa suna cikin ɓata bayyananniya. |
|
458 | 3 | 165 | أولما أصابتكم مصيبة قد أصبتم مثليها قلتم أنى هذا قل هو من عند أنفسكم إن الله على كل شيء قدير |
| | | Shin kuma a lõkacin da wata masĩfa, haƙĩƙa, ta sãme ku alhãli kuwa kun sãmar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rãyukanku yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kõme, Mai ĩkon yi ne. |
|
459 | 3 | 166 | وما أصابكم يوم التقى الجمعان فبإذن الله وليعلم المؤمنين |
| | | Kuma abin da ya sãme ku a rãnar haɗuwar jama'a biyu, to, da izinin Allah ne, kuma dõmin (Allah) Ya san mũminai (na gaskiya). |
|
460 | 3 | 167 | وليعلم الذين نافقوا وقيل لهم تعالوا قاتلوا في سبيل الله أو ادفعوا قالوا لو نعلم قتالا لاتبعناكم هم للكفر يومئذ أقرب منهم للإيمان يقولون بأفواههم ما ليس في قلوبهم والله أعلم بما يكتمون |
| | | Kuma dõmin Ya san waɗanda suka yi munãfunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yãƙi a cikin hanyar Allah, kõ kuwa ku tunkuɗe." Suka ce: "Dã mun san (yadda ake) yãƙi dã mun bĩ ku." Sũ zuwa ga kãfirci a rãnar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga ĩmãni. Sunã cẽwa da bãkunansu abin da bã shi ne a cikin zukãtansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓõyewa. |
|
461 | 3 | 168 | الذين قالوا لإخوانهم وقعدوا لو أطاعونا ما قتلوا قل فادرءوا عن أنفسكم الموت إن كنتم صادقين |
| | | Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Dã sun yi mana ɗã'a, dã ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rãyukanku, idan kun kasance mãsu gaskiya." |
|
462 | 3 | 169 | ولا تحسبن الذين قتلوا في سبيل الله أمواتا بل أحياء عند ربهم يرزقون |
| | | Kada ka yi zaton waɗanda aka kashe a cikin hanyar Allah matattu ne. A'a, rãyayyu ne su, a wurin bangijinsu. Ana ciyar da su. |
|
463 | 3 | 170 | فرحين بما آتاهم الله من فضله ويستبشرون بالذين لم يلحقوا بهم من خلفهم ألا خوف عليهم ولا هم يحزنون |
| | | Suna mãsu farin ciki sabõda abin da Allah Ya bã su daga falalarSa, kuma suna yin bushãra ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Bãbu tsõro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba." |
|