نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4530 | 46 | 20 | ويوم يعرض الذين كفروا على النار أذهبتم طيباتكم في حياتكم الدنيا واستمتعتم بها فاليوم تجزون عذاب الهون بما كنتم تستكبرون في الأرض بغير الحق وبما كنتم تفسقون |
| | | Kuma rãnar da ake gitta waɗanda suka kãflrta a kan wutã (a ce musu): "Kun tafiyar da abũbuwanku na jin dãɗi a cikin rayuwarku ta dũniya, kuma kun nẽmi jin dãdi da su, to, ayau anã sãka muka da azãbar wulãkanci, dõmin abin da kuka kasance kanã yi na gmian kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, kuma dõmin abin da kuka kasance kuna yi na fãsiƙansi." |
|
4531 | 46 | 21 | واذكر أخا عاد إذ أنذر قومه بالأحقاف وقد خلت النذر من بين يديه ومن خلفه ألا تعبدوا إلا الله إني أخاف عليكم عذاب يوم عظيم |
| | | Kuma ka ambaci ɗan'uwan Ãdãwa a lõkacin da ya yi gargaɗi ga mutãnensa, a Tuddan Rairayi, alhãli kuwa waɗansu mãsu gargaɗi sun shũɗe agaba gare shi da bãya gare shi (da cẽwa) "Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah. Lalle nĩ inã tsõrata muku azãbar yini mai girma." |
|
4532 | 46 | 22 | قالوا أجئتنا لتأفكنا عن آلهتنا فأتنا بما تعدنا إن كنت من الصادقين |
| | | Suka ce: "Shin, kã zo mana ne dõmin ka karkatar da mu daga gumãkaumu? To, ka zo mana da abin da kake yi mana wa'adin, idan kã kasance daga mãsu gaskiya." |
|
4533 | 46 | 23 | قال إنما العلم عند الله وأبلغكم ما أرسلت به ولكني أراكم قوما تجهلون |
| | | Ya ce: "Ilimi a wurin Allah kawai yake, kuma inã iyar maku abin da aka aiko ni da shi, kuma amma inã ganin, kũ, wasu mutãne ne, kunã jãhiltar gaskiya." |
|
4534 | 46 | 24 | فلما رأوه عارضا مستقبل أوديتهم قالوا هذا عارض ممطرنا بل هو ما استعجلتم به ريح فيها عذاب أليم |
| | | To, a lõkacin da suka ga azãbar, kumar hadari mai fuskantar rãfukansu, suka ce: "Wannan hadari ne mai yi mana ruwa. Ã'a, shĩ na abin da kuke nẽman gaggawar saukarsa; Iska ce, a cikinta akwai wata azaba mai raɗaɗi. |
|
4535 | 46 | 25 | تدمر كل شيء بأمر ربها فأصبحوا لا يرى إلا مساكنهم كذلك نجزي القوم المجرمين |
| | | Tanã darkake kõwane abu da umurnin Ubangijinta. Sai suka wãyi gari, bã a ganin kõme fãce gidãjensu. Kamar wannan ne Muke sãka wa mutãne mãsu laifi. |
|
4536 | 46 | 26 | ولقد مكناهم فيما إن مكناكم فيه وجعلنا لهم سمعا وأبصارا وأفئدة فما أغنى عنهم سمعهم ولا أبصارهم ولا أفئدتهم من شيء إذ كانوا يجحدون بآيات الله وحاق بهم ما كانوا به يستهزئون |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun ba su ĩko ga abin da ba Mubã ku ĩko gare shi ba, kuma Muka sanya musu wani irin jĩ da gani dazukãta. Sai dai jnsu bai amfãne su ba, kuma zukãtansu ba su amfãne su ba ga kõme, dõmin sun kasance sunã musu game da ãyõyin Allah, kuma abin da suka kasance sunã aikatãwa na izgili game da shi ya wajaba a gare su. |
|
4537 | 46 | 27 | ولقد أهلكنا ما حولكم من القرى وصرفنا الآيات لعلهم يرجعون |
| | | Kuma ne, lalle haƙĩƙa, Mun halakar da abin da yake kẽwayenku na alƙaryu kuma Muka jujjũya ãyõyi, tsammãninsu zã su kõmo. |
|
4538 | 46 | 28 | فلولا نصرهم الذين اتخذوا من دون الله قربانا آلهة بل ضلوا عنهم وذلك إفكهم وما كانوا يفترون |
| | | To, don mẽne ne waɗanda suka riƙa, baicin Allah, abũbuwan yi. wa baiko, gumaka, ba su taimake su ba? Ã'a, sun ɓace musu Kuma wannan shi ne ƙiren ƙaryarsu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa. |
|
4539 | 46 | 29 | وإذ صرفنا إليك نفرا من الجن يستمعون القرآن فلما حضروه قالوا أنصتوا فلما قضي ولوا إلى قومهم منذرين |
| | | Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi. |
|