نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4504 | 45 | 31 | وأما الذين كفروا أفلم تكن آياتي تتلى عليكم فاستكبرتم وكنتم قوما مجرمين |
| | | Kuma amma waɗanda suka kãfirtã (Allah zai ce musu): "Shin, ãyõyĩNã ba su kasance anã karãnta su ã kanku ba sai kuka kangare, Kuma kuka kasance mutãne mãsu laifi?" |
|
4505 | 45 | 32 | وإذا قيل إن وعد الله حق والساعة لا ريب فيها قلتم ما ندري ما الساعة إن نظن إلا ظنا وما نحن بمستيقنين |
| | | "Kuma idan aka ce, lalle wa'ãdin Allah gaskiya ne, kuma Sa'a, bãbu shakka a cikinta sai kuka ce, 'Ba mu san abin da ake cẽwa Sa'a ba, bã mu zãto (game da ita) fãce zato mai rauni, Kuma ba mu zama mãsu yaƙni ba."' |
|
4506 | 45 | 33 | وبدا لهم سيئات ما عملوا وحاق بهم ما كانوا به يستهزئون |
| | | Kuma mũnanan abin da suka aikata ya bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili ya wajaba a kansu. |
|
4507 | 45 | 34 | وقيل اليوم ننساكم كما نسيتم لقاء يومكم هذا ومأواكم النار وما لكم من ناصرين |
| | | Kuma aka ce: "A yau zã Mu manta da ku, kamar yadda kuka manta da gamuwa da yininku wannan. Kuma mãkõmarku wutã ce, Kuma bã ku da waɗansu mãsu taimako. |
|
4508 | 45 | 35 | ذلكم بأنكم اتخذتم آيات الله هزوا وغرتكم الحياة الدنيا فاليوم لا يخرجون منها ولا هم يستعتبون |
| | | "Wancan dõmin lalle kũ, kun riƙi ãyõyin Allah da izgili, Kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe ku. To, a yau bã zã su fita daga gare ta ba, Kuma bã zã su zama waɗanda ake nẽman yardarsu ba." |
|
4509 | 45 | 36 | فلله الحمد رب السماوات ورب الأرض رب العالمين |
| | | Sabõda haka, gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin sammai, kuma Ubangijin ƙasã, Ubangijin halittu. |
|
4510 | 45 | 37 | وله الكبرياء في السماوات والأرض وهو العزيز الحكيم |
| | | Kuma gare Shi girma yake, a cikin sammai da ƙasã, kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Hikima. |
|
4511 | 46 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم حم |
| | | Ḥ. M̃. |
|
4512 | 46 | 2 | تنزيل الكتاب من الله العزيز الحكيم |
| | | Saukar da littafi daga Allah, Mabuwãyi, Mai hikima yake. |
|
4513 | 46 | 3 | ما خلقنا السماوات والأرض وما بينهما إلا بالحق وأجل مسمى والذين كفروا عما أنذروا معرضون |
| | | Ba Mu halitta sammai da ƙasa ba, da abin da ke tsakãninsu, fãce da gaskiya da wani ajali ambatacce, kuma waɗanda suka kãfirta, mãsu bijirẽwa ne daga abin da aka yi musu gargaɗi (da shi). |
|