نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4465 | 44 | 51 | إن المتقين في مقام أمين |
| | | Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce. |
|
4466 | 44 | 52 | في جنات وعيون |
| | | A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari. |
|
4467 | 44 | 53 | يلبسون من سندس وإستبرق متقابلين |
| | | Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna. |
|
4468 | 44 | 54 | كذلك وزوجناهم بحور عين |
| | | Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyaun idãnu, mãsu girmansu. |
|
4469 | 44 | 55 | يدعون فيها بكل فاكهة آمنين |
| | | Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro). |
|
4470 | 44 | 56 | لا يذوقون فيها الموت إلا الموتة الأولى ووقاهم عذاب الجحيم |
| | | Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm. |
|
4471 | 44 | 57 | فضلا من ربك ذلك هو الفوز العظيم |
| | | Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma. |
|
4472 | 44 | 58 | فإنما يسرناه بلسانك لعلهم يتذكرون |
| | | Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa. |
|
4473 | 44 | 59 | فارتقب إنهم مرتقبون |
| | | Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne. |
|
4474 | 45 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم حم |
| | | Ḥ. M̃. |
|