نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4448 | 44 | 34 | إن هؤلاء ليقولون |
| | | Lalle waɗannan mutãne, haƙĩka, sunã cẽwa, |
|
4449 | 44 | 35 | إن هي إلا موتتنا الأولى وما نحن بمنشرين |
| | | "Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba." |
|
4450 | 44 | 36 | فأتوا بآبائنا إن كنتم صادقين |
| | | "Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya." |
|
4451 | 44 | 37 | أهم خير أم قوم تبع والذين من قبلهم أهلكناهم إنهم كانوا مجرمين |
| | | shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi. |
|
4452 | 44 | 38 | وما خلقنا السماوات والأرض وما بينهما لاعبين |
| | | Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã. |
|
4453 | 44 | 39 | ما خلقناهما إلا بالحق ولكن أكثرهم لا يعلمون |
| | | Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba. |
|
4454 | 44 | 40 | إن يوم الفصل ميقاتهم أجمعين |
| | | Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya. |
|
4455 | 44 | 41 | يوم لا يغني مولى عن مولى شيئا ولا هم ينصرون |
| | | Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba. |
|
4456 | 44 | 42 | إلا من رحم الله إنه هو العزيز الرحيم |
| | | fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai. |
|
4457 | 44 | 43 | إن شجرت الزقوم |
| | | Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã), |
|