نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4434 | 44 | 20 | وإني عذت بربي وربكم أن ترجمون |
| | | "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." |
|
4435 | 44 | 21 | وإن لم تؤمنوا لي فاعتزلون |
| | | "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." |
|
4436 | 44 | 22 | فدعا ربه أن هؤلاء قوم مجرمون |
| | | Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. |
|
4437 | 44 | 23 | فأسر بعبادي ليلا إنكم متبعون |
| | | (Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku.)" |
|
4438 | 44 | 24 | واترك البحر رهوا إنهم جند مغرقون |
| | | "Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa." |
|
4439 | 44 | 25 | كم تركوا من جنات وعيون |
| | | Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari. |
|
4440 | 44 | 26 | وزروع ومقام كريم |
| | | Da shuke-shuke da matsayi mai kyau. |
|
4441 | 44 | 27 | ونعمة كانوا فيها فاكهين |
| | | Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu. |
|
4442 | 44 | 28 | كذلك وأورثناها قوما آخرين |
| | | Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam. |
|
4443 | 44 | 29 | فما بكت عليهم السماء والأرض وما كانوا منظرين |
| | | Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba. |
|