نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4427 | 44 | 13 | أنى لهم الذكرى وقد جاءهم رسول مبين |
| | | Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? |
|
4428 | 44 | 14 | ثم تولوا عنه وقالوا معلم مجنون |
| | | Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." |
|
4429 | 44 | 15 | إنا كاشفو العذاب قليلا إنكم عائدون |
| | | Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). |
|
4430 | 44 | 16 | يوم نبطش البطشة الكبرى إنا منتقمون |
| | | Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. |
|
4431 | 44 | 17 | ولقد فتنا قبلهم قوم فرعون وجاءهم رسول كريم |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu. |
|
4432 | 44 | 18 | أن أدوا إلي عباد الله إني لكم رسول أمين |
| | | (Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku." |
|
4433 | 44 | 19 | وأن لا تعلوا على الله إني آتيكم بسلطان مبين |
| | | "Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne." |
|
4434 | 44 | 20 | وإني عذت بربي وربكم أن ترجمون |
| | | "Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni." |
|
4435 | 44 | 21 | وإن لم تؤمنوا لي فاعتزلون |
| | | "Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni." |
|
4436 | 44 | 22 | فدعا ربه أن هؤلاء قوم مجرمون |
| | | Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi. |
|