نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4421 | 44 | 7 | رب السماوات والأرض وما بينهما إن كنتم موقنين |
| | | (Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka). |
|
4422 | 44 | 8 | لا إله إلا هو يحيي ويميت ربكم ورب آبائكم الأولين |
| | | Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko. |
|
4423 | 44 | 9 | بل هم في شك يلعبون |
| | | A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka. |
|
4424 | 44 | 10 | فارتقب يوم تأتي السماء بدخان مبين |
| | | Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne. |
|
4425 | 44 | 11 | يغشى الناس هذا عذاب أليم |
| | | Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi. |
|
4426 | 44 | 12 | ربنا اكشف عنا العذاب إنا مؤمنون |
| | | Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne. |
|
4427 | 44 | 13 | أنى لهم الذكرى وقد جاءهم رسول مبين |
| | | Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)? |
|
4428 | 44 | 14 | ثم تولوا عنه وقالوا معلم مجنون |
| | | Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa ne, mahaukaci." |
|
4429 | 44 | 15 | إنا كاشفو العذاب قليلا إنكم عائدون |
| | | Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin). |
|
4430 | 44 | 16 | يوم نبطش البطشة الكبرى إنا منتقمون |
| | | Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne. |
|