نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
443 | 3 | 150 | بل الله مولاكم وهو خير الناصرين |
| | | Ã'a, Allah ne Majiɓincinku kuma ShĨ ne Mafi alhẽrin matai maka. |
|
444 | 3 | 151 | سنلقي في قلوب الذين كفروا الرعب بما أشركوا بالله ما لم ينزل به سلطانا ومأواهم النار وبئس مثوى الظالمين |
| | | Zã Mu jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta sabõda shirkin da suka yi da Allah gãme da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makõmarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzãlumai! |
|
445 | 3 | 152 | ولقد صدقكم الله وعده إذ تحسونهم بإذنه حتى إذا فشلتم وتنازعتم في الأمر وعصيتم من بعد ما أراكم ما تحبون منكم من يريد الدنيا ومنكم من يريد الآخرة ثم صرفكم عنهم ليبتليكم ولقد عفا عنكم والله ذو فضل على المؤمنين |
| | | Kuma lalle ne haƙĩƙa Allah Yã yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lõkacin da kuka kãsa, kuma kuka yi jãyayya a cikin al'amarin, kuma kuka sãɓã a bãyan (Allah) Ya nũna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lãhĩra. Sa'an nan kuma Ya jũyar da ku daga gare su, dõmin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Ya yãfe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga mũminai. |
|
446 | 3 | 153 | إذ تصعدون ولا تلوون على أحد والرسول يدعوكم في أخراكم فأثابكم غما بغم لكيلا تحزنوا على ما فاتكم ولا ما أصابكم والله خبير بما تعملون |
| | | A lõkacin da kuke hawan dũtse, gudãne. Kuma ba ku karkata a kan kõwa ba, alhãli kuwa Manzon Allah nã kiran ku a cikin na ƙarshenku. Sa'an nan (Allah) Ya sãkã muku da baƙin ciki a tãre da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya sãme ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa. |
|
447 | 3 | 154 | ثم أنزل عليكم من بعد الغم أمنة نعاسا يغشى طائفة منكم وطائفة قد أهمتهم أنفسهم يظنون بالله غير الحق ظن الجاهلية يقولون هل لنا من الأمر من شيء قل إن الأمر كله لله يخفون في أنفسهم ما لا يبدون لك يقولون لو كان لنا من الأمر شيء ما قتلنا هاهنا قل لو كنتم في بيوتكم لبرز الذين كتب عليهم القتل إلى مضاجعهم وليبتلي الله ما في صدوركم وليمحص ما في قلوبكم والله عليم بذات الصدور |
| | | Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bãyan baƙin cikin; gyangyaɗi yanã rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rãyukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da bã shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cẽwa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓõyẽwa a cikin zukatansu, abin da bã su bayyana shi a gare ka. Suna cẽwa: "Da munã da wani abu daga al'amarin dã ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Kõ dã kun kasance a cikin gidãjenku, dã waɗanda aka rubũta musu kisa sun fita zuwa ga wurãren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu yã auku ne) dõmin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirãzanku. Kuma dõmin Ya tsarkake abin da ke cikin zukãtanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. |
|
448 | 3 | 155 | إن الذين تولوا منكم يوم التقى الجمعان إنما استزلهم الشيطان ببعض ما كسبوا ولقد عفا الله عنهم إن الله غفور حليم |
| | | Lalle ne waɗanda suka jũya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talãlãɓantar da su, sabõda sãshen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yãfe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gãfara Mai haƙuri. |
|
449 | 3 | 156 | يا أيها الذين آمنوا لا تكونوا كالذين كفروا وقالوا لإخوانهم إذا ضربوا في الأرض أو كانوا غزى لو كانوا عندنا ما ماتوا وما قتلوا ليجعل الله ذلك حسرة في قلوبهم والله يحيي ويميت والله بما تعملون بصير |
| | | Yã ku waɗanda suka yi ĩmani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kãfirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa kõ kuwa suka kasance a wurin yãƙi: "Dã sun kasance a wurinmu dã ba su mutun ba, kuma dã ba a, kashe su ba." (Wannan kuwa) Dõmin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadãma a cikin zukãtansu. Kuma Allah ne Yake rãyarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani ne. |
|
450 | 3 | 157 | ولئن قتلتم في سبيل الله أو متم لمغفرة من الله ورحمة خير مما يجمعون |
| | | Kuma lalle ne idan aka kashe, ku a cikin hanyar Allah, ko kuwa kuka mutu, haƙĩƙa, gãfara daga Allah da rahama ne mafi alhẽri daga abin da suke tãrãwa. |
|
451 | 3 | 158 | ولئن متم أو قتلتم لإلى الله تحشرون |
| | | Kuma lalle ne idan kun mutu ko kuwa aka kashe ku, haƙĩƙa, zuwa ga Allah ake tãra ku. |
|
452 | 3 | 159 | فبما رحمة من الله لنت لهم ولو كنت فظا غليظ القلب لانفضوا من حولك فاعف عنهم واستغفر لهم وشاورهم في الأمر فإذا عزمت فتوكل على الله إن الله يحب المتوكلين |
| | | Sabõda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma dã kã kasance mai hushi mai kaurin zuciya, dã sun wãtse daga gẽfenka. Sai ka yãfe musu laifinsu, kuma ka nẽma musu gãfara, kuma ka yi shãwara da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dõgara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son mãsu tawakkali. |
|