نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4410 | 43 | 85 | وتبارك الذي له ملك السماوات والأرض وما بينهما وعنده علم الساعة وإليه ترجعون |
| | | Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurinSa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku. |
|
4411 | 43 | 86 | ولا يملك الذين يدعون من دونه الشفاعة إلا من شهد بالحق وهم يعلمون |
| | | Kuma waɗanda suke kira baicinSa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane (da haka). |
|
4412 | 43 | 87 | ولئن سألتهم من خلقهم ليقولن الله فأنى يؤفكون |
| | | Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su? |
|
4413 | 43 | 88 | وقيله يا رب إن هؤلاء قوم لا يؤمنون |
| | | Kuma da (ilmin) maganarSa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba." |
|
4414 | 43 | 89 | فاصفح عنهم وقل سلام فسوف يعلمون |
| | | To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani. |
|
4415 | 44 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم حم |
| | | Ḥ. M̃. |
|
4416 | 44 | 2 | والكتاب المبين |
| | | Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani. |
|
4417 | 44 | 3 | إنا أنزلناه في ليلة مباركة إنا كنا منذرين |
| | | Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi. |
|
4418 | 44 | 4 | فيها يفرق كل أمر حكيم |
| | | A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne. |
|
4419 | 44 | 5 | أمرا من عندنا إنا كنا مرسلين |
| | | Umurni na daga wurinMu. Lalle Mũ ne Muka kasanceMãsu aikãwã. |
|