نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4389 | 43 | 64 | إن الله هو ربي وربكم فاعبدوه هذا صراط مستقيم |
| | | "Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya." |
|
4390 | 43 | 65 | فاختلف الأحزاب من بينهم فويل للذين ظلموا من عذاب يوم أليم |
| | | Sai ƙungiyõyi suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi! |
|
4391 | 43 | 66 | هل ينظرون إلا الساعة أن تأتيهم بغتة وهم لا يشعرون |
| | | Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba. |
|
4392 | 43 | 67 | الأخلاء يومئذ بعضهم لبعض عدو إلا المتقين |
| | | Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne). |
|
4393 | 43 | 68 | يا عباد لا خوف عليكم اليوم ولا أنتم تحزنون |
| | | Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba. |
|
4394 | 43 | 69 | الذين آمنوا بآياتنا وكانوا مسلمين |
| | | Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyinMu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah). |
|
4395 | 43 | 70 | ادخلوا الجنة أنتم وأزواجكم تحبرون |
| | | Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku. |
|
4396 | 43 | 71 | يطاف عليهم بصحاف من ذهب وأكواب وفيها ما تشتهيه الأنفس وتلذ الأعين وأنتم فيها خالدون |
| | | Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne. |
|
4397 | 43 | 72 | وتلك الجنة التي أورثتموها بما كنتم تعملون |
| | | Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa. |
|
4398 | 43 | 73 | لكم فيها فاكهة كثيرة منها تأكلون |
| | | Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci. |
|