نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4364 | 43 | 39 | ولن ينفعكم اليوم إذ ظلمتم أنكم في العذاب مشتركون |
| | | Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba. |
|
4365 | 43 | 40 | أفأنت تسمع الصم أو تهدي العمي ومن كان في ضلال مبين |
| | | Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna? |
|
4366 | 43 | 41 | فإما نذهبن بك فإنا منهم منتقمون |
| | | To, kõ dai Mu tafi da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu. |
|
4367 | 43 | 42 | أو نرينك الذي وعدناهم فإنا عليهم مقتدرون |
| | | Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne. |
|
4368 | 43 | 43 | فاستمسك بالذي أوحي إليك إنك على صراط مستقيم |
| | | Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciyl. |
|
4369 | 43 | 44 | وإنه لذكر لك ولقومك وسوف تسألون |
| | | Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku. |
|
4370 | 43 | 45 | واسأل من أرسلنا من قبلك من رسلنا أجعلنا من دون الرحمن آلهة يعبدون |
| | | Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu?" |
|
4371 | 43 | 46 | ولقد أرسلنا موسى بآياتنا إلى فرعون وملئه فقال إني رسول رب العالمين |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu." |
|
4372 | 43 | 47 | فلما جاءهم بآياتنا إذا هم منها يضحكون |
| | | To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyinMu, sai gã su sunã yi musu dãriya. |
|
4373 | 43 | 48 | وما نريهم من آية إلا هي أكبر من أختها وأخذناهم بالعذاب لعلهم يرجعون |
| | | Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa. |
|