نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4332 | 43 | 7 | وما يأتيهم من نبي إلا كانوا به يستهزئون |
| | | Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili. |
|
4333 | 43 | 8 | فأهلكنا أشد منهم بطشا ومضى مثل الأولين |
| | | Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe. |
|
4334 | 43 | 9 | ولئن سألتهم من خلق السماوات والأرض ليقولن خلقهن العزيز العليم |
| | | Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su." |
|
4335 | 43 | 10 | الذي جعل لكم الأرض مهدا وجعل لكم فيها سبلا لعلكم تهتدون |
| | | Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa.' |
|
4336 | 43 | 11 | والذي نزل من السماء ماء بقدر فأنشرنا به بلدة ميتا كذلك تخرجون |
| | | Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari). |
|
4337 | 43 | 12 | والذي خلق الأزواج كلها وجعل لكم من الفلك والأنعام ما تركبون |
| | | Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa. |
|
4338 | 43 | 13 | لتستووا على ظهوره ثم تذكروا نعمة ربكم إذا استويتم عليه وتقولوا سبحان الذي سخر لنا هذا وما كنا له مقرنين |
| | | Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba. |
|
4339 | 43 | 14 | وإنا إلى ربنا لمنقلبون |
| | | "Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu." |
|
4340 | 43 | 15 | وجعلوا له من عباده جزءا إن الإنسان لكفور مبين |
| | | Kuma suka sanya Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin. |
|
4341 | 43 | 16 | أم اتخذ مما يخلق بنات وأصفاكم بالبنين |
| | | Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza? |
|