نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
433 | 3 | 140 | إن يمسسكم قرح فقد مس القوم قرح مثله وتلك الأيام نداولها بين الناس وليعلم الله الذين آمنوا ويتخذ منكم شهداء والله لا يحب الظالمين |
| | | Idan wani mĩki ya shãfe ku, to, lalle ne, wani mĩki kamarsa ya shãfi mutãnen, kuma waɗancan kwãnaki Muna sarrafa su a tsakãnin mutãne dõmin Allah Ya san waɗanda suka yi ĩmãni kuma Ya sãmi mãsu shahãda daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzãlumai. |
|
434 | 3 | 141 | وليمحص الله الذين آمنوا ويمحق الكافرين |
| | | Kuma dõmin Allah Ya ɗauraye waɗanda suka yi ĩmãni, kuma Ya ƙõƙe kãfirai. |
|
435 | 3 | 142 | أم حسبتم أن تدخلوا الجنة ولما يعلم الله الذين جاهدوا منكم ويعلم الصابرين |
| | | Ko kun yi zaton ku shiga Aljanna alhãli kuwa Allah bai bãda sanin waɗanda suka yĩ jihãdi daga gare ku ba, kuma Ya san mãsu haƙuri? |
|
436 | 3 | 143 | ولقد كنتم تمنون الموت من قبل أن تلقوه فقد رأيتموه وأنتم تنظرون |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa kun kasance kuna gũrin mutuwa tun a gabãnin ku haɗu da ita, to lalle ne kun gan ta, alhãli kuwa kuna kallo. |
|
437 | 3 | 144 | وما محمد إلا رسول قد خلت من قبله الرسل أفإن مات أو قتل انقلبتم على أعقابكم ومن ينقلب على عقبيه فلن يضر الله شيئا وسيجزي الله الشاكرين |
| | | Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shũɗe a gabãninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, zã kujũya a kan dugaduganku? To, wanda ya jũya a kan dugadugansa, bã zai cũci Allah da kõme ba. Kuma Allah zai sãka wa mãsu gõdiya. |
|
438 | 3 | 145 | وما كان لنفس أن تموت إلا بإذن الله كتابا مؤجلا ومن يرد ثواب الدنيا نؤته منها ومن يرد ثواب الآخرة نؤته منها وسنجزي الشاكرين |
| | | Kuma bã ya yiwuwa ga wani rai ya mutu fãce da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon dũniya Muna bã shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lãhira Muna bã shi daga gare ta. Kuma zã Mu sãka wa mãsu godiya. |
|
439 | 3 | 146 | وكأين من نبي قاتل معه ربيون كثير فما وهنوا لما أصابهم في سبيل الله وما ضعفوا وما استكانوا والله يحب الصابرين |
| | | Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yãƙi, akwai jama'a mãsu yawa tãre da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son mãsu haƙuri. |
|
440 | 3 | 147 | وما كان قولهم إلا أن قالوا ربنا اغفر لنا ذنوبنا وإسرافنا في أمرنا وثبت أقدامنا وانصرنا على القوم الكافرين |
| | | Kuma bãbu abin da ya kasance maganarsu fãce faɗarsu cẽwa: "Ya Ubangijinmu! Ka gãfarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutãnen nan kãfirai." |
|
441 | 3 | 148 | فآتاهم الله ثواب الدنيا وحسن ثواب الآخرة والله يحب المحسنين |
| | | Allah Yã sãka musu da sakamakon dũniya da kuma kyakkyawan sakamakon Lãhira. Kuma Allah yana son mãsu kyautatãwa. |
|
442 | 3 | 149 | يا أيها الذين آمنوا إن تطيعوا الذين كفروا يردوكم على أعقابكم فتنقلبوا خاسرين |
| | | Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Idan kun yi ɗa'aga waɗanda suka kãfirta zã su mayar da ku a kan dugãduganku, har ku jũya kunã mãsu hasãra. |
|