نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4319 | 42 | 47 | استجيبوا لربكم من قبل أن يأتي يوم لا مرد له من الله ما لكم من ملجإ يومئذ وما لكم من نكير |
| | | Ku karɓã wa Ubangijinku tun gabãnin wani yini ya zo, bãbu makawa gare shi daga Allah, bã ku da wata mafaka a rãnar nan, kuma bã ku iya yin wani musu. |
|
4320 | 42 | 48 | فإن أعرضوا فما أرسلناك عليهم حفيظا إن عليك إلا البلاغ وإنا إذا أذقنا الإنسان منا رحمة فرح بها وإن تصبهم سيئة بما قدمت أيديهم فإن الإنسان كفور |
| | | To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne. |
|
4321 | 42 | 49 | لله ملك السماوات والأرض يخلق ما يشاء يهب لمن يشاء إناثا ويهب لمن يشاء الذكور |
| | | Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda Yake so. |
|
4322 | 42 | 50 | أو يزوجهم ذكرانا وإناثا ويجعل من يشاء عقيما إنه عليم قدير |
| | | Kõ kuma Ya haɗa su maza da mãtã, kuma Yanã sanya wanda Ya so bakarãre. Lalle shi, Mai ilmi ne, Mai ĩkon yi. |
|
4323 | 42 | 51 | وما كان لبشر أن يكلمه الله إلا وحيا أو من وراء حجاب أو يرسل رسولا فيوحي بإذنه ما يشاء إنه علي حكيم |
| | | Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana fãce da wahayi, kõ daga bãYan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima. |
|
4324 | 42 | 52 | وكذلك أوحينا إليك روحا من أمرنا ما كنت تدري ما الكتاب ولا الإيمان ولكن جعلناه نورا نهدي به من نشاء من عبادنا وإنك لتهدي إلى صراط مستقيم |
| | | Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩnMu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya. |
|
4325 | 42 | 53 | صراط الله الذي له ما في السماوات وما في الأرض ألا إلى الله تصير الأمور |
| | | Hanyar Allah wanda ke da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. To, zuwa ga Allah kawai al'amura ke kõmãwa. |
|
4326 | 43 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم حم |
| | | Ḥ. M̃. |
|
4327 | 43 | 2 | والكتاب المبين |
| | | Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani. |
|
4328 | 43 | 3 | إنا جعلناه قرآنا عربيا لعلكم تعقلون |
| | | Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta. |
|