نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4300 | 42 | 28 | وهو الذي ينزل الغيث من بعد ما قنطوا وينشر رحمته وهو الولي الحميد |
| | | Kuma Shĩ ne ke sassaukar da girgije (ruwa) a bãyan sun yanke ƙauna kuma Yana wãtsa rahamarSa, alhãli kuwa Shĩ ne Majiɓinci, Mai gõdiya. |
|
4301 | 42 | 29 | ومن آياته خلق السماوات والأرض وما بث فيهما من دابة وهو على جمعهم إذا يشاء قدير |
| | | Kuma akwai daga ãyõyinSa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya wãtsa a cikinsu na dabba alhãli kuwa Shĩ Mai ĩko ne ga tãra su, a lõkacin da Yake so. |
|
4302 | 42 | 30 | وما أصابكم من مصيبة فبما كسبت أيديكم ويعفو عن كثير |
| | | Kuma abin da ya sãme ku na wata masifa, to, game da abin da hannãyenku suka sana' anta ne kuma (Alah) Yanã Yafẽwar (waɗansu laifuffuka) mãsu yawa. |
|
4303 | 42 | 31 | وما أنتم بمعجزين في الأرض وما لكم من دون الله من ولي ولا نصير |
| | | Kuma ba ku zama mãsu buwãya ba a cikin ƙasa kuma bã ku da wani majiɓinci, wanin Allah, kuma bã ku da wani mataimaki. |
|
4304 | 42 | 32 | ومن آياته الجوار في البحر كالأعلام |
| | | Kuma akwai daga ãyõyinsa, jirãge mãsu gudãna a cikin tẽku kamar duwãtsu. |
|
4305 | 42 | 33 | إن يشأ يسكن الريح فيظللن رواكد على ظهره إن في ذلك لآيات لكل صبار شكور |
| | | Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun, Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya. |
|
4306 | 42 | 34 | أو يوبقهن بما كسبوا ويعف عن كثير |
| | | Kõ Ya halakã su (sũ jirãgen) sabõda abin da mãsu su suka sanã'anta, alhãli kuwa Yanã yãfe (laifuffuka) mãsu yawa. |
|
4307 | 42 | 35 | ويعلم الذين يجادلون في آياتنا ما لهم من محيص |
| | | Kuma dõmin waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyinMu su sani (cẽwa) bã su da wata mafaka. |
|
4308 | 42 | 36 | فما أوتيتم من شيء فمتاع الحياة الدنيا وما عند الله خير وأبقى للذين آمنوا وعلى ربهم يتوكلون |
| | | Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai. |
|
4309 | 42 | 37 | والذين يجتنبون كبائر الإثم والفواحش وإذا ما غضبوا هم يغفرون |
| | | Kuma waɗanda ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfãsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sunã gãfartawa. |
|