نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4288 | 42 | 16 | والذين يحاجون في الله من بعد ما استجيب له حجتهم داحضة عند ربهم وعليهم غضب ولهم عذاب شديد |
| | | Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani. |
|
4289 | 42 | 17 | الله الذي أنزل الكتاب بالحق والميزان وما يدريك لعل الساعة قريب |
| | | Allah ne Wanda Ya saukar da Littãfi da gaskiya, da sikeli. Kuma me ya sanar da kai (cẽwa anã) tsammãnin Sa'ar kusa take? |
|
4290 | 42 | 18 | يستعجل بها الذين لا يؤمنون بها والذين آمنوا مشفقون منها ويعلمون أنها الحق ألا إن الذين يمارون في الساعة لفي ضلال بعيد |
| | | Waɗanda ba su yi ĩmãnida ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa, sunã a cikin ɓata Mai nĩsa. |
|
4291 | 42 | 19 | الله لطيف بعباده يرزق من يشاء وهو القوي العزيز |
| | | Allah Mai tausasãwa ne ga bãyinsa. Yanã azurta wanda yake so, alhãli kuma Shĩ ne Maiƙarfi, Mabuwãyi. |
|
4292 | 42 | 20 | من كان يريد حرث الآخرة نزد له في حرثه ومن كان يريد حرث الدنيا نؤته منها وما له في الآخرة من نصيب |
| | | Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira. |
|
4293 | 42 | 21 | أم لهم شركاء شرعوا لهم من الدين ما لم يأذن به الله ولولا كلمة الفصل لقضي بينهم وإن الظالمين لهم عذاب أليم |
| | | Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi. |
|
4294 | 42 | 22 | ترى الظالمين مشفقين مما كسبوا وهو واقع بهم والذين آمنوا وعملوا الصالحات في روضات الجنات لهم ما يشاءون عند ربهم ذلك هو الفضل الكبير |
| | | Kanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma. |
|
4295 | 42 | 23 | ذلك الذي يبشر الله عباده الذين آمنوا وعملوا الصالحات قل لا أسألكم عليه أجرا إلا المودة في القربى ومن يقترف حسنة نزد له فيها حسنا إن الله غفور شكور |
| | | Wancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyinSa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya. |
|
4296 | 42 | 24 | أم يقولون افترى على الله كذبا فإن يشإ الله يختم على قلبك ويمح الله الباطل ويحق الحق بكلماته إنه عليم بذات الصدور |
| | | Kõ zã su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata. |
|
4297 | 42 | 25 | وهو الذي يقبل التوبة عن عباده ويعفو عن السيئات ويعلم ما تفعلون |
| | | Kuma Shi ne ke karɓar tũba daga bãyinSa, kuma Yanã Yafe ƙananan laifuffuka, alhãli kuwa Yanã sanin abin da kuke aikatãwa. |
|