نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4212 | 40 | 79 | الله الذي جعل لكم الأنعام لتركبوا منها ومنها تأكلون |
| | | Allah ne Wanda Ya sanya muku dabbõbi dõmin ku hau daga gare su, kuma daga gare su kuke ci. |
|
4213 | 40 | 80 | ولكم فيها منافع ولتبلغوا عليها حاجة في صدوركم وعليها وعلى الفلك تحملون |
| | | Kuma kunã da abũbuwan amfãni a cikinsu, kuma dõmin ku isar da wata buƙãta, a cikin ƙirãzanku a kansu kuma a kansu da a kan jirãge ake, ɗaukar ku. |
|
4214 | 40 | 81 | ويريكم آياته فأي آيات الله تنكرون |
| | | Kuma Ya nũna muku ayõyinSa. To, wane ãyõyin Allah kuke musu? |
|
4215 | 40 | 82 | أفلم يسيروا في الأرض فينظروا كيف كان عاقبة الذين من قبلهم كانوا أكثر منهم وأشد قوة وآثارا في الأرض فما أغنى عنهم ما كانوا يكسبون |
| | | Ashe fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasã ba, dõmin su dũba yadda ãƙibar waɗanda ke a gabãninsu ta kasance? Sun kasance mafi yawa daga gare su. Kuma sun fi tsananin ƙarfi, da (yawan) gurãbun sanã'õ'i a cikin ƙasã. To, abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su ba. |
|
4216 | 40 | 83 | فلما جاءتهم رسلهم بالبينات فرحوا بما عندهم من العلم وحاق بهم ما كانوا به يستهزئون |
| | | A lõkacin da Manzanninsu suka jẽ musu da hujjõji bayyanannu, suka yi farin ciki da abin da ke wurinsu na ilmi kuma abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi ya wajaba a kansu. |
|
4217 | 40 | 84 | فلما رأوا بأسنا قالوا آمنا بالله وحده وكفرنا بما كنا به مشركين |
| | | Sa'an nan a lõkacin da suka ga azãbarMu, suka ce: "Mun yi ĩmãni da Allah, Shi kaɗai, kuma mun kãfirta da abin da muka kasance munã shirki da shi." |
|
4218 | 40 | 85 | فلم يك ينفعهم إيمانهم لما رأوا بأسنا سنت الله التي قد خلت في عباده وخسر هنالك الكافرون |
| | | To ĩmaninsu bai kasance yanã amfaninsu ba a lõkacin da suka ga azãbarMu. Hanyar Allah wadda ta gabãta a cikin bãyinSa. Kuma kãfirai sun yi hasãra a can. |
|
4219 | 41 | 1 | بسم الله الرحمن الرحيم حم |
| | | Ḥ. M̃. |
|
4220 | 41 | 2 | تنزيل من الرحمن الرحيم |
| | | Saukarwa (da Alƙur' ãni) dãga Mai rahama ne, Mai jin ƙai. |
|
4221 | 41 | 3 | كتاب فصلت آياته قرآنا عربيا لقوم يعلمون |
| | | Littãfi ne, an bayyana ãyõyinsa daki-daki, yanã abin karantãwa na Lãrabci, dõmin mutãnen dake sani |
|