نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4194 | 40 | 61 | الله الذي جعل لكم الليل لتسكنوا فيه والنهار مبصرا إن الله لذو فضل على الناس ولكن أكثر الناس لا يشكرون |
| | | Allah ne Wanda Ya sanya muku dare dõmin ku natsu a cikinsa, da rãna mai gãnarwa. Lalle Allah, haƙĩƙa, Ma'abũcin falala ne a kan mutãne, kuma amma mafi yawan mutãne bã su gõdẽwa. |
|
4195 | 40 | 62 | ذلكم الله ربكم خالق كل شيء لا إله إلا هو فأنى تؤفكون |
| | | Wancan shine Allah Ubangijinku, Mahaliccin dukan kõme, bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku? |
|
4196 | 40 | 63 | كذلك يؤفك الذين كانوا بآيات الله يجحدون |
| | | Kamar haka ake karkatar da waɗanda suka kasance sunã jãyayya game da ãyõyin Allah. |
|
4197 | 40 | 64 | الله الذي جعل لكم الأرض قرارا والسماء بناء وصوركم فأحسن صوركم ورزقكم من الطيبات ذلكم الله ربكم فتبارك الله رب العالمين |
| | | Allah ne Ya sanya muku kasã tabbatacciya, da sama ginanniya, kuma Ya sũranta ku, sa'an nan Ya kyautata sũrõrinku,, kuma Ya azurta ku daga abũbuwa mãsu dãɗi. Wancan Shĩne Allah Ubangijinku. To, albarkar Allah Ubangijin halittu tã bayyana. |
|
4198 | 40 | 65 | هو الحي لا إله إلا هو فادعوه مخلصين له الدين الحمد لله رب العالمين |
| | | Shĩ ne Mai rai, bãbu abin bautãwa fãce Shi. Sabõda haka ku kira Shi, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi. Gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu. |
|
4199 | 40 | 66 | قل إني نهيت أن أعبد الذين تدعون من دون الله لما جاءني البينات من ربي وأمرت أن أسلم لرب العالمين |
| | | Ka ce: "Lalle nĩ, an hana ni in bauta wa waɗanda kuke kira waɗansun Allah a lõkacin da hujjõji bayyanannu suka zo mini daga Ubangijina, kuma an umurce ni in sallama ga Ubangijin halittu." |
|
4200 | 40 | 67 | هو الذي خلقكم من تراب ثم من نطفة ثم من علقة ثم يخرجكم طفلا ثم لتبلغوا أشدكم ثم لتكونوا شيوخا ومنكم من يتوفى من قبل ولتبلغوا أجلا مسمى ولعلكم تعقلون |
| | | Shĩ ne Wanda Ya halitta ku daga turɓãya, sa'an nan daga maniyyi, sa'an nan daga sãren jini, sa'an nan Ya fitar da ku kunã jãrĩri, sa'an nan dõmin ku isa ga cikar ƙarfinku sa'an nan dõmin ku kasance tsõfaffi, kuma daga cikinku, akwai wanda ake karɓar ransa a gabãnin haka, kuma dõmin ku isa ga ajali ambatacce, kuma dammãninku ko zã ku hankalta. |
|
4201 | 40 | 68 | هو الذي يحيي ويميت فإذا قضى أمرا فإنما يقول له كن فيكون |
| | | Shi ne Wanda ke rayarwa kuma Yana kashewa. To, idan Ya hukunta wani al'amari, to, Yana cewa kawai gare shi, ka kasance sai yana kasancewa (kamar yadda ake bukatar sa.) |
|
4202 | 40 | 69 | ألم تر إلى الذين يجادلون في آيات الله أنى يصرفون |
| | | Ashe, ba ka gani ba ga waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyin Allah, yadda ake karkatar da su? |
|
4203 | 40 | 70 | الذين كذبوا بالكتاب وبما أرسلنا به رسلنا فسوف يعلمون |
| | | Waɗanda suka ƙaryata, game da Littãfin, kuma da abin da Muka aika Manzanninmu da shi. To, za su sani. |
|