نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4179 | 40 | 46 | النار يعرضون عليها غدوا وعشيا ويوم تقوم الساعة أدخلوا آل فرعون أشد العذاب |
| | | Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, "Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba." |
|
4180 | 40 | 47 | وإذ يتحاجون في النار فيقول الضعفاء للذين استكبروا إنا كنا لكم تبعا فهل أنتم مغنون عنا نصيبا من النار |
| | | Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna (mabiya) su ce wa waɗanda suka kangara (shugabanni), "Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã?" |
|
4181 | 40 | 48 | قال الذين استكبروا إنا كل فيها إن الله قد حكم بين العباد |
| | | Waɗanda suka kangara suka ce: "Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyinSa." |
|
4182 | 40 | 49 | وقال الذين في النار لخزنة جهنم ادعوا ربكم يخفف عنا يوما من العذاب |
| | | Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama, "Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana, a yini ɗaya, daga azãba." |
|
4183 | 40 | 50 | قالوا أولم تك تأتيكم رسلكم بالبينات قالوا بلى قالوا فادعوا وما دعاء الكافرين إلا في ضلال |
| | | Suka ce: "Ashe, Manzanninku ba su jẽ muku da hujjõji bayyanannu ba?" Suka ce: "Na'am, sun jẽ!" Suka ce: "To, ku rõƙa." Kuma rõƙon kãfirai bai zamo ba fãce a cikin ɓata. |
|
4184 | 40 | 51 | إنا لننصر رسلنا والذين آمنوا في الحياة الدنيا ويوم يقوم الأشهاد |
| | | Lalle Mũ, hakĩka, Munã taimakon ManzanninMu da waɗanda suka yi ĩmãni, a cikin rãyuwar dũniya da rãnar da shaidu ke tsayãwa. |
|
4185 | 40 | 52 | يوم لا ينفع الظالمين معذرتهم ولهم اللعنة ولهم سوء الدار |
| | | Rãnar da uzurin azzãlumai bã ya amfãninsu, kuma sunã da la'ana, kuma sunã da mũnin gida. |
|
4186 | 40 | 53 | ولقد آتينا موسى الهدى وأورثنا بني إسرائيل الكتاب |
| | | Kuma lalle haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã shiriya, kuma Mun gãdar da Banĩ Isrã'ĩla Littãfi. |
|
4187 | 40 | 54 | هدى وذكرى لأولي الألباب |
| | | Shiryarwa da tunãwa ga ma'abũta hankali. |
|
4188 | 40 | 55 | فاصبر إن وعد الله حق واستغفر لذنبك وسبح بحمد ربك بالعشي والإبكار |
| | | Sabõda haka, ka yi haƙuri, lalle wa'adin Allah gaskiya ne. Kuma ka nẽmi gãfara ga zunubinka, kuma ka yi tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinka, maraice da kuma wãyẽwar sãfiya. |
|