نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
413 | 3 | 120 | إن تمسسكم حسنة تسؤهم وإن تصبكم سيئة يفرحوا بها وإن تصبروا وتتقوا لا يضركم كيدهم شيئا إن الله بما يعملون محيط |
| | | Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne. |
|
414 | 3 | 121 | وإذ غدوت من أهلك تبوئ المؤمنين مقاعد للقتال والله سميع عليم |
| | | Kuma a lõkacin da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani. |
|
415 | 3 | 122 | إذ همت طائفتان منكم أن تفشلا والله وليهما وعلى الله فليتوكل المؤمنون |
| | | A lõkacin da ƙungiyõyi biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara. |
|
416 | 3 | 123 | ولقد نصركم الله ببدر وأنتم أذلة فاتقوا الله لعلكم تشكرون |
| | | Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa. |
|
417 | 3 | 124 | إذ تقول للمؤمنين ألن يكفيكم أن يمدكم ربكم بثلاثة آلاف من الملائكة منزلين |
| | | A lõkacin da kake cẽwa ga mũminai, "Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku?" |
|
418 | 3 | 125 | بلى إن تصبروا وتتقوا ويأتوكم من فورهم هذا يمددكم ربكم بخمسة آلاف من الملائكة مسومين |
| | | "Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma." |
|
419 | 3 | 126 | وما جعله الله إلا بشرى لكم ولتطمئن قلوبكم به وما النصر إلا من عند الله العزيز الحكيم |
| | | Kuma Allah bai sanya shi ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima. |
|
420 | 3 | 127 | ليقطع طرفا من الذين كفروا أو يكبتهم فينقلبوا خائبين |
| | | Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi. |
|
421 | 3 | 128 | ليس لك من الأمر شيء أو يتوب عليهم أو يعذبهم فإنهم ظالمون |
| | | Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne. |
|
422 | 3 | 129 | ولله ما في السماوات وما في الأرض يغفر لمن يشاء ويعذب من يشاء والله غفور رحيم |
| | | Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. |
|