نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4115 | 39 | 57 | أو تقول لو أن الله هداني لكنت من المتقين |
| | | "Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'" |
|
4116 | 39 | 58 | أو تقول حين ترى العذاب لو أن لي كرة فأكون من المحسنين |
| | | "Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'" |
|
4117 | 39 | 59 | بلى قد جاءتك آياتي فكذبت بها واستكبرت وكنت من الكافرين |
| | | "Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai." |
|
4118 | 39 | 60 | ويوم القيامة ترى الذين كذبوا على الله وجوههم مسودة أليس في جهنم مثوى للمتكبرين |
| | | Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai? |
|
4119 | 39 | 61 | وينجي الله الذين اتقوا بمفازتهم لا يمسهم السوء ولا هم يحزنون |
| | | Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba. |
|
4120 | 39 | 62 | الله خالق كل شيء وهو على كل شيء وكيل |
| | | Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme. |
|
4121 | 39 | 63 | له مقاليد السماوات والأرض والذين كفروا بآيات الله أولئك هم الخاسرون |
| | | Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra. |
|
4122 | 39 | 64 | قل أفغير الله تأمروني أعبد أيها الجاهلون |
| | | Ka ce: "Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai!" |
|
4123 | 39 | 65 | ولقد أوحي إليك وإلى الذين من قبلك لئن أشركت ليحبطن عملك ولتكونن من الخاسرين |
| | | Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra." |
|
4124 | 39 | 66 | بل الله فاعبد وكن من الشاكرين |
| | | Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya. |
|