نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4109 | 39 | 51 | فأصابهم سيئات ما كسبوا والذين ظلموا من هؤلاء سيصيبهم سيئات ما كسبوا وما هم بمعجزين |
| | | Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba. |
|
4110 | 39 | 52 | أولم يعلموا أن الله يبسط الرزق لمن يشاء ويقدر إن في ذلك لآيات لقوم يؤمنون |
| | | Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni. |
|
4111 | 39 | 53 | قل يا عبادي الذين أسرفوا على أنفسهم لا تقنطوا من رحمة الله إن الله يغفر الذنوب جميعا إنه هو الغفور الرحيم |
| | | Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai." |
|
4112 | 39 | 54 | وأنيبوا إلى ربكم وأسلموا له من قبل أن يأتيكم العذاب ثم لا تنصرون |
| | | "Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba." |
|
4113 | 39 | 55 | واتبعوا أحسن ما أنزل إليكم من ربكم من قبل أن يأتيكم العذاب بغتة وأنتم لا تشعرون |
| | | "Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba." |
|
4114 | 39 | 56 | أن تقول نفس يا حسرتا على ما فرطت في جنب الله وإن كنت لمن الساخرين |
| | | "Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili!"' |
|
4115 | 39 | 57 | أو تقول لو أن الله هداني لكنت من المتقين |
| | | "Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa.'" |
|
4116 | 39 | 58 | أو تقول حين ترى العذاب لو أن لي كرة فأكون من المحسنين |
| | | "Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa.'" |
|
4117 | 39 | 59 | بلى قد جاءتك آياتي فكذبت بها واستكبرت وكنت من الكافرين |
| | | "Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai." |
|
4118 | 39 | 60 | ويوم القيامة ترى الذين كذبوا على الله وجوههم مسودة أليس في جهنم مثوى للمتكبرين |
| | | Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai? |
|