نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4068 | 39 | 10 | قل يا عباد الذين آمنوا اتقوا ربكم للذين أحسنوا في هذه الدنيا حسنة وأرض الله واسعة إنما يوفى الصابرون أجرهم بغير حساب |
| | | Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba. |
|
4069 | 39 | 11 | قل إني أمرت أن أعبد الله مخلصا له الدين |
| | | Ka ce: "Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi. |
|
4070 | 39 | 12 | وأمرت لأن أكون أول المسلمين |
| | | "Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah)." |
|
4071 | 39 | 13 | قل إني أخاف إن عصيت ربي عذاب يوم عظيم |
| | | Ka ce: "Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma." |
|
4072 | 39 | 14 | قل الله أعبد مخلصا له ديني |
| | | Ka ce: "Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi. |
|
4073 | 39 | 15 | فاعبدوا ما شئتم من دونه قل إن الخاسرين الذين خسروا أنفسهم وأهليهم يوم القيامة ألا ذلك هو الخسران المبين |
| | | "To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna." |
|
4074 | 39 | 16 | لهم من فوقهم ظلل من النار ومن تحتهم ظلل ذلك يخوف الله به عباده يا عباد فاتقون |
| | | Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyinSa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa. |
|
4075 | 39 | 17 | والذين اجتنبوا الطاغوت أن يعبدوها وأنابوا إلى الله لهم البشرى فبشر عباد |
| | | Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa. |
|
4076 | 39 | 18 | الذين يستمعون القول فيتبعون أحسنه أولئك الذين هداهم الله وأولئك هم أولو الألباب |
| | | Waɗanda ke sauraren magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali, |
|
4077 | 39 | 19 | أفمن حق عليه كلمة العذاب أفأنت تنقذ من في النار |
| | | Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã? |
|