نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4029 | 38 | 59 | هذا فوج مقتحم معكم لا مرحبا بهم إنهم صالو النار |
| | | Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne. |
|
4030 | 38 | 60 | قالوا بل أنتم لا مرحبا بكم أنتم قدمتموه لنا فبئس القرار |
| | | Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar). |
|
4031 | 38 | 61 | قالوا ربنا من قدم لنا هذا فزده عذابا ضعفا في النار |
| | | Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã." |
|
4032 | 38 | 62 | وقالوا ما لنا لا نرى رجالا كنا نعدهم من الأشرار |
| | | Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?" |
|
4033 | 38 | 63 | أتخذناهم سخريا أم زاغت عنهم الأبصار |
| | | "Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?" |
|
4034 | 38 | 64 | إن ذلك لحق تخاصم أهل النار |
| | | Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã. |
|
4035 | 38 | 65 | قل إنما أنا منذر وما من إله إلا الله الواحد القهار |
| | | Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa." |
|
4036 | 38 | 66 | رب السماوات والأرض وما بينهما العزيز الغفار |
| | | "Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara." |
|
4037 | 38 | 67 | قل هو نبأ عظيم |
| | | Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma". |
|
4038 | 38 | 68 | أنتم عنه معرضون |
| | | "Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi!" |
|