نتائج البحث: 6236
|
ترتيب الآية | رقم السورة | رقم الآية | الاية |
4025 | 38 | 55 | هذا وإن للطاغين لشر مآب |
| | | Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma. |
|
4026 | 38 | 56 | جهنم يصلونها فبئس المهاد |
| | | Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita. |
|
4027 | 38 | 57 | هذا فليذوقوه حميم وغساق |
| | | Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini. |
|
4028 | 38 | 58 | وآخر من شكله أزواج |
| | | Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i. |
|
4029 | 38 | 59 | هذا فوج مقتحم معكم لا مرحبا بهم إنهم صالو النار |
| | | Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne. |
|
4030 | 38 | 60 | قالوا بل أنتم لا مرحبا بكم أنتم قدمتموه لنا فبئس القرار |
| | | Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar). |
|
4031 | 38 | 61 | قالوا ربنا من قدم لنا هذا فزده عذابا ضعفا في النار |
| | | Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã." |
|
4032 | 38 | 62 | وقالوا ما لنا لا نرى رجالا كنا نعدهم من الأشرار |
| | | Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai?" |
|
4033 | 38 | 63 | أتخذناهم سخريا أم زاغت عنهم الأبصار |
| | | "Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne?" |
|
4034 | 38 | 64 | إن ذلك لحق تخاصم أهل النار |
| | | Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã. |
|